Akalla dakarun sojin Janhuriyar Nijar 11 ne suka mutu a wani hari da yan bindiga suka zuwa wani kauye mai suna Dagne a jiya juma’a.
Sanarwa daga hukumomin kasar na nuni cewa 9 daga cikin dakarun sojin dake wurin suka samu rauni.
Tun ranar juma’a gwamnatin ta ayyana zaman makoki na kwanaki biyu,yayin da Shugaban kasar tareda rakiyar ministan tsaron jamhuriuyar ta Nijar ya kai ziyara banibangou don jajintawa mutanen da suka rasa na su a wannan hari.
A wani labarin na daban kasar Nijar makwonni biyu da suka gabata ta ayyana dokar ta baci a wasu yankunan yammacin kasar dake makwabtaka da kasar Mali sakamakon hare-haren ta’addanci da masu jihadi ke ta kaiwa.
A zaman taron minstocin mako, hukumomin Nijar sun sanar da tsawaita dokar ta baci a yankunan Ouallam, Ayorou, Bankilare, Abala da Banibangou dake jihar Tillabery dama wasu yankuna dake jihar Tahoua da suka hada da Tassara da Tillia.
Gani wa’adin ya zo karshe , zaman taron na Ministoci ya amince da tsawaita dokar na watani uku domin sake dawowa da zaman lafiya a wadanan yankuna da yan ta’ada ke ta kai hari dama kasha mutane.