Daga dukkan alamu gwamna Wike na jihar Ribas ya gama yanke shawara kan ɗan takarar da zai marawa baya.
Gwamna Wike yayi alƙawarin bayyanawa ‘yan Najeriya sunan ɗan takarar da zai tallata ga ƴan Najeriya a watan Janairu.
Wani babban jigo a jam’iyya mai mulki ta APC yace Wike da ƴan tawagar sa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu za su marawa baya.
Akwai alamun dake nuna cewa gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, daga karshe zai nuna goyon bayan sa ga Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, a watan Janairun 2023.
Hakan na zuwa ne bayan da jagororin jam’iyyar APC suka nuna ƙwarin guiwar su kan tawagar G5 ta jam’iyyar PDP wacce Wike ke jagoranta, zata marawa Tinubu baya a zaɓen shugaban ƙasa na shekarar 2023. Rahoton jaridar Legit.ng ya tabbatar.
A satin da ya gabata, gwamna Wike yayi alƙawarin bayyana ɗan takarar shugaban ƙasar da zai yiwa yaƙin neman zaɓe a watan Janairu kafin zuwan babban zaɓe na 2023.
Gwamnan ya kuma bayyana cewa zai zaga lungu da saƙo na ƙasar nan domin yiwa ɗan takarar yaƙin neman zaɓe domin yasa ƴan Najeriya su ƙada masa ƙuri’un su.
Da yake magana a ranar Lahadi, wani babban jigo a jam’iyyar wanda ya nemi da a sakaya sunan sa, yace jagororin jam’iyyar ta APC na da ƙwarin guiwa kan cewa Wike da ƴan tawagar sa Tinubu za su marawa baya.
Mu a jam’iyyar APC, muna da cikakken ƙwarin guiwa kan cewa ƴan tawagar G5 Asiwaju za su marawa baya.
Akwai ƴan takarar shugaban ƙasa mutum uku waɗanda ke daga kan gaba.
Sun nuna gabaɗaya ba sa tare da Atiku Abubakar na PDP.
Tawagar yaƙin neman zaɓen Atiku har bugar ƙirji sun yi kan cewa za su ci zaɓe ba tare da goyon bayan ƴan tawagar G5 ba.
Kada ka manta, Atiku kuma ya ƙyale Seyi Makinde.
Sannan ya sanar Ademola Adeleke a matsayin shugaban kwamitin yaƙin neman zaɓen sa na yankin Kudu maso Yamma.
Fafutukar G5 Ta Wuce Babban Zaben 2023, Gwamnan Abiya Ya Yi Karin Haske
A wani labarin kuma gwamnan jihar Abiya yayi ƙarin haske dangane da tafiyar G5 suke yi domin ganin an samu daidaito da adalci.
Gwamna Okezie Ikpeazu yana daga cikin mambobin tawagar G5 wacce ke ƙarƙashin jagorancin gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike.
Gwamnan yace ba zasu yi kasa a guiwa ba wajen tabbatar da gaskiya da adalci har gaban zaben 2023.