Wani tsohon soja ya amince cewa ya taimaka wajen jigilar ‘yan ta’addan da suka kashe jagoran juyin juya halin Burkina Faso, Thomas Sankara, a shari’ar da aka fara shekaru 34 bayan kisan gillar.
Elise ya amince da haka ne yayın da yake bada shaida ga kotun soji da ke birnin Ouagadogou, gaban al’ummar Burkina Faso da ke bin shari’ar sau da kafa, wadanda ke fatan samun karin haske kan kisan gillar.
Duk da ya amince da jigilar wadanda suka aikata kissan gillar, ya ce ba ya cikin wadanda suka kitsa lamarin, sannan kuma bai cikin masu harbi a lokacin juyin mulkin.
Mutane 14 aka gurfanar gaban kotun kan kisan gillar da aka yi a shekarar 1987 lokacin da aka kashe Sankara da wasu mutane 12 yayin da suke wani babban taro na gwamnati.
Cikin wadanda ake tuhuma har da babban aminin Sankara, Blaise Compaore, wanda ya hau karagar mulki bayan kisan gillar.
Kuma tsohon sojin da ya amince da taimaka wa kisan gillar, ya tabbatar da kasance da wasu sojojin a gidan Blaise Compaore a ranar 15 ga watan Oktober shekarar 1987 da aka gudanar da juyin mulkin.