‘Yan majalisar wakilai daga jam’iyyar PDP sun yi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da yayi murabus.
‘Yan majalisa sun bayyana hakane inda suka bayyana dalilin cewa, kashe-kashe yayi yawa a Najeriya.
O.K Chinda wanda shine shugaban ‘yan majalisar na PDP yace ‘yan ta’adda sun mamaye Najeriya.
Yace amma abin takaici shine Janar din da ya bugi kirjin cewa zai shiga gaba a yi yaki dashi yanzu ya bace an rasa inda yake.
Yace yanzu Najeriya ta zama dandalin kashe mutane, dan hakane suke kiran shugaban kasar ya sauka kawai.