Sabon kocin Tottenham Antonio Conte ya fara jagorantar kungiyar da kafar dama, bayan da ya samu nasara kan Vitesse da kwallaye 3-2 a wasan farko da kungiyar ta fafata a karkashinsa na gasar Europa a daren ranar Alhamis.
A mintuna 45 na farkon wasan na daren Alhamis da suka fafata sai da magoya bayan Tottenham suka yi tsayuwar ban girma ga Conte ganin yadda cikin mintuna 28 kungiyar tasa dake wasa a gida ta samu nasarar jefa kwallaye 3 a ragar Vitesse.
A shekarar 2016 dai Antonio Conte ya samu nasara a wasan farko da ya jagoranci kungiyar Chelsea, daga bisani kuma ya samu nasara lashe wasanni 13 a jere, wanda kuma a waccan lokacin kungiyar ta Tottenham ad a yanzu yake horaswa ce ta kawo karshen nasarorin da ya jera da kwallaye 2-0.
A wani labarin na daban kungiyar kwallon kafa ta Tottenham ta fara tattaunawa da tsohon manajan Chelsea Antonio Conte a wani yunkuri na bashi ragamar horar da kungiyar bayan korar manajanta Nuno Espirito da safiyar yau litinin sakamakon rashin abin kirkin da kungiyar ke ci gaba da yi a wannan kaka.
Sanarwar Tottenham ta ce shugaban kungiyar Deniel Levy da daraktanta Fabio Paratici na fatan gaggauta maye gurbin Espirito gabanin wasan da ke tunkaro kungiyar a nan gaba, inda tuni suka fara ganawa da Conte.
Korar Esprito dai na zuwa ne watanni 4 kacal bayan karbar ragamar horar da kungiyar wadda ta gaza tabuka abin kirki tun bayan tafiyar Mauricio Pochettino.
Tottenham ta sanar da cewa daga yanzu zuwa gobe talata ne za ta sanar da magajin Esprito wanda ta bada tabbacin ya iya zama Conte.
Conte mai shekaru 52 dai ya bar aikin horar da Inter Milan ne makwanni kalilan bayan nasararsa ta dagewa kungiyar kofin Serie A.
Haka zalika a lokacinsa na horar da Chelsea ya yi nasarar dage kofin Firimiya da na FA amma kuma kungiyar ta raba gari da shi a shekarar 2018 bayan gaza tabuka abin kirki a shekarar.