Wani binciken kungiyar CDD a Najeriya ya bayyana cewar rashin hukunci da nuna kabilanci tare da talauci ne suka zafafa ayyukan ta’addancin da suka mamaye yankunan karkarar Jihohin dake arewa maso yammacin kasar.
Kungiyar tace ya zuwa wannan lokaci, wadannan ‘Yan bindiga sun kashe akalla fararen hula 12,000, yayin da suka tilastawa sama da miliyan guda tserewa daga gidajen su domin samun mafaka.
CDD tace tashe tashen hankulan da ake samu a jihohin dake arewa maso yamma da ya fantsama zuwa Jihar Neja dake yankin arewa ta tsakiya, matsalar da ta rikide ta zama yaki yadda ‘Yan ta’adda ke kai hari akan cibiyoyin soji da jiragen kasa da kuma hari akan matafiya a manyan hanyoyin kasar.
Cibiyar tace duk da yake ana cigaba da mahawara akan bukatar ‘Yan ta’addan da kuma abinda ke basu kwarin guiwa, CDD tayi watsi da zargin cewar mayakan boko haram da ‘Yan siyasa da Fulani na tallafawa ‘Yan bindigar.
Cibiyar tace babu yadda za’a takaita abinda ya haifar da tashin hankalin zuwa matsala guda, domin kuwa dole sai an duba batutuwa da dama da suka hada da tattalin arziki da siyasa da kuma matsalolin rayuwar yau da kullum.
CDD tace rashin hukunci akan wadanda suka aikata manyan laifuffuka da cin hanci da rashawa daga bangaren shari’a tare da bangaren ‘Yan Sanda na daga cikin dalilan da suka sa wasu daukar makamai domin samarwa kansu mafita.
Cibiyar tace kungiyoyin Sakai da ake kafawa a wasu garuruwa domin kare jama’a suma sun taka rawa wajen daukar doka a hannun su, inda suke wuce makada da rawa wajen kashe Fulanin da basu ji ba, basu gani ba, musamman a Jihar Zamfara.
CDD ta kara da cewar talauci ya kuma taimaka wajen sanya wasu mutane daukar matakai domin rashin sana’ar da za suyi su samu kudade.
Cibiyar tace babu yadda za’a yi nasarar shawo kan wannan matsala sai dole an samu hadin kan shugabannin da matsalar ta shafa da kuma karfin guiwa daga bangaren gwamnati wajen duba matsalolin tsaro da zummar shawo kan su.
CDD ta yi misali da yadda aka kashe Buharin Daji, daya daga cikin manyan Yan bindigar Jihar Zamfara, wanda matakin ya haifar da rarrabuwar ‘yayan kungiyar sa da kuma ingiza matsalar maimakon shawo kan ta.
Cibiyar tace duk wani mataki da za’a dauka na dakile wannan matsala sai ya shafi sake fasalin aikin tsaro da kuma dawo da yarda tsakanin su da jama’ar dake karkara.