Atiku Abubakar ya samu gayyata daga gwamnatin Burtaniya, an tattauna dashi kan wasu batutuwa.
Jam’iyyar PDP ta fito ta yi bayani, ta bayyana gaskiyar abin da dan takarar na PDP ya tattauna da Burtaniya.
Hakazalika, PDP ta ce akwai haske ga Atiku a zaben shugaban kasa da za a yi nan da wata guda a Najeriya.
Majalisar kamfen din takarar shugaban kasa ta jam’iyyar PDP ta bayyana dalilin da yasa gwamnatin kasar Burtaniya ta gayyaci Atiku don tattaunawa dashi, New Telegraph ta ruwaito.
A cewar majalisar, an gayyaci Atiku ne domin tattauna batutuwan da suka shafi gamayya da hadin gwiwa tsakanin Najeriya da Burtaniya a nan gaba idan ya gaji Buhari.
Wannan na fitowa ne daga daraktan yada labaran majalisar, Otunba Dele Momodu a cikin wani sako da ya bayar a jiya Talata 10 ga watan Janairu.
Akwai yiwuwar Atiku ya lashe zabe, inji Dele Momodu Momodu ya kuma bayyana cewa, akwai haske mai kyau game da nasarar Atiku a zaben da za a gudanar a cikin watan Fabrairu mai zuwa, rahoton Vanguard.
A cewar sakon nasa: “Majiya ciki ta naqalto cewa, zaben ciki gida a na gwamnatin Burtaniya ya nuna AA (Atiku Abubakar) ne dan takarar da kan gaba kuma akwai yiwuwar aiki kafada-kafada dashi don amfanin kasashen biyu.
“Wannan na da matukar muhimmanci domin Burtaniya na son habakawa da fadada alakar kasuwanci da Najeriya.”
Rikicin da ke gaban Atiku a matakin jam’iyya Duk da wannan, har yanzu dan takarar na shugaban kasa a PDP na ci gaba da fuskantar barazana da koma baya a jam’iyyar, kasancewar akwai wasu jiga-jigan jam’iyyar da ke adawa dashi.
Gamayyar gwamnonin G-5 na ci gaba da nuna adawa da shugabancin PDP a matakin kasa, kana sun ce babu ruwansu da Atiku.
Gwamnonin dai burinsu shine; su ga an tsige Ayu Iyorchia ammatsayin shugaban jam’iyyar na kasa tare da ba wani dan yankin Kudu.
Burtaniya ba za ta tsoma baki a zaben bana ba A tun farko kun ji cewa, kasar Burtaniya ta ce ba za ta sanya baki a zaben da za a gudanar a Najeriya ba kwata-kwata.
Wannan na fitowa ne daga bakin Ms Catriona Laing, babbar kwamishiniyar Burtaniya a Najeriya lokacin da take magana game da zaben na bana.
Ta kuma bayyana cewa, kasar ta Turai za ta tsaya ne tsaka-tsaki kan dukkan abubuwan da za su faru a zaben. Asali: Legit.ng Kasance mutumin farko da zai samu labarai.