Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kama hanyar zuwa birnin London don duba lafiyarsa. balaguron da zai dauke shi tsawon makwanni 2.
Ko a watan Maris din 2021 sai da shugaba Muhammadu Buhari ya harzaya London wajen duba lafiyarsa ko da ya ke an dakatar da makamanciyar ziyarar a watan Yunin shekarar.
Sanarwar fadar shugaban na Najeriya, ta ce tawagar shugaba Muhammadu Buhari za ta bar kasar a yau talata tare da rakiyar ministan waje Geoffrey Onyeama dana muhalli Sharon Ikeazor baya ga Babagana Monguno da kuma Ambasada Ahmed Rufa’I Abubakar sai Abike Dabiri-Erewa.
Buhari zai kasance a taron na Majalisar Dinkin Duniya har zuwa ranar 4 ga watan nan inda zai gana da shugaban Kenya Uhuru Kenyatta.
A wani labariin na daban ‘Yan Najeriya mazauna Birtaniya sun gudanar da zanga zangar lumana a birnin London domin nuna bacin ran su da abinda suka kira ci gaba da tabarbarewar tsaron da ya addabi Yankin arewacin kasar sakamakon kashe jama’a ba tare da kaukautawa ba.
Daya daga cikin wadanda suka shirya zanga zangar Fareed Lawal Bello ya shaidawa RFI Hausa cewar duk da yake ba’a zaune suke a Najeriya ba yanzu, amma sun damu da halin da take ciki ganin yadda a kullum suke karanta labarin yadda ‘Yan bindiga ke kai hari suna kashe jama’a da jikkata su da kuma sace dukiyar su ko kuma garkuwa da su domin karbar kudin fansa.
Bello yace basu gamsu da rawar da gwamnati tace tana takawa akan lamarin ba, ko kuma kokarin da tace tana yi akan matsalar, saboda haka suna bukatar kara kaimi domin kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Ya kara da cewa shugaba Buhari ko damuwa baya yi wajen zuwa ya jajantawa jama’ar da aka kaiwa hari ko zasu ji sanyin lamarin, kamar abinda ya faru lokacin da ‘Yan bindiga suka kona mutane sama da 40 a cikin mota a jihar Sokoto.
Bello yace idan wannan al’amari yana faruwa a karkashin shugaban da ya fito daga yankin arewacin Najeriya ba tare da dakile shi ba, gobe idan aka samu sauyin mulkin kasar ya koma wani bangare ba’a san abinda zai faru a ‘yankin ba.
A karshe yace idan wadanda ke shugabancin bangarori daban daban a Najeriya suka ki daukar matakan da suka dace na kare rayuka da dukiyoyin jama’a, su kwan da sanin cewar a ranar gobe kiyama zasu amsa tambayoyi a gaban Ubangiji dangane da rawar da kowanne daga cikin su ya taka na shugabancin da aka dora musu.
Daga cikin wadanda suka yiwa gangamin jawabi harda fitaccen ‘dan Jarida kuma mawallafin Daily Nigerian Jaafar Jaafar da Lauya Bulama Bukarti.