Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rantsar da kwamishinonin hukumar zaben kasar guda 3 inda ya bukace su da su jajirce wajen bada gudumawar tabbatar da zabe mai inganci a cikin kasar.
Daga cikin su akwai Farfesa Muhammad Sani Adam wanda ke wakiltar Yankin Arewa ta Tsakiya da Dr Baba Bila dake wakiltar Arewa ta Gabas sai kuma Farfesa Abdullahi Abdul dake wakiltar Arewa ta Yamma.
Bikin rantsuwar ya gudana ne kafin taron mako-mako na majalisar ministocin kasar da aka saba gudanarwa kowacce ranar laraba a fadar shugaban kasar.
Cikin wadanda suka halarci bikin rantsuwar harda mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo da Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Gida Mustapha da ministan shari’a Abubakar Malami.
Ana saran kwamishinonin da buhari ya nada su bada gudumawa wajen shirin zaben shekarar 2023 da zai gudana.
A wani labarin na daban kamfanin dillancin labaran alfurat News ya bayar da rahoton cewa, ministan harkokin cikin gida na kasar Iraki Usman alghanimi ya bayyana cewa, a halin yanzu jami’an tsaro sun shirya tsaf domin gudanar da ayyukan tsaro a lokacin tarukan arba’in nan da ‘yan kwanaki masu zuwa.
Ya ce halin yanzu rundunar tsaro ta hadin gwiwa ta riga ta gama kammala tsare-tsarenta a bangaren ayyukan tsaro a lokacin wadannan taruka, inda jami’an dubu 20 ne aka ware domin wannan aiki.
Ministan harkokin cikin gidan na Iraki ya ce, ya zama wajibi su dauki irin wadannan kwararan matakan na tsaro, bisa la’akari da matsalolin da aka rika samu a lokutan baya na hare-haren ‘yan ta’adda lokacin tarukan addini a kasar.
Yanzu haka dai jama’a daga sassa daban-daban na kasar Iraki sun fara yin tattaki zuwa birnin Karbala domin halartar tarukan na arba’in da za su gudana a ranar 20 ga wannan wata na Safar da muke ciki.