Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa shugaban Faransa Emmanuel Macron akan fadada harkokin kasuwanci tsakanin kasashen biyu, yayin da ya jaddada hadin kan Najeriya da kasar wajen murkushe kungiyoyin ‘Yan ta’adda tare da Faransa.
Yayin da ya ziyarci fadar shugaban Faransa inda ya gana da shugaba Macron, Buhari yace ziyarar da Macron ya kai Najeriya a shekarar 2018 ta bude kofofin ci gaba ta hanyar sana’oi, yadda harkokin kasuwanci suka habaka, musamman kafa kungiyar zuba jari tsakanin kasashen biyu.
Shugaban Najeriya ya yaba da rawar da shugaba Macron ya taka wajen bunkasa dangantakar kasashen biyu lokacin da ya ziyarci birnin Lagos a shekarar 2018 wadda ta bashi damar samar da yanayin da aka kafa kungiyar Yan kasuwanci da janyo manyan yan kasuwar kasashen guda biyu wanda shugaban kamfanin BUA Abdusamad Rabiu ke jagoranci.
Dangane da batun tsaro kuma, Buhari ya jinjinawa Faransa akan aniyar ta na tabbatar da zaman lafiya a yankin Sahel da kuma Yankin Tafkin Chadi, wadanda suka taimaka wajen yaki da ta’addanci da kuma tsatsauran ra’ayi.
Shugaba buhari ya bayyana kaurar baki da kuma safarar mutane a matsayin manyan kalubalen da suka damu kasashen biyu, tare da gungun masu aikata laifuffuka na kasa da kasa dake gudanar da harkokin su a nahiyar Afirka da Turai, inda suke tagayyara marasa karfi, yayin da ya jaddada aniyar su ta ci gaba da aiki tare da Faransa wajen murkushe su.
Buhari yace Najeriya da Faransa na da damar fadada dangantakar su ta hanyar tintibar juna a matakin ministoci, yayin da ya bayyana kasar a matsayin kawa abokiyar tafiya dangane da ci gaban kasashen Afirka.
Shugaban ya kuma yaba da hadin kai tsakanin Hukumomin ilimin kasashen biyu wanda ke nuna ci gaban da ake samu wajen ilmintar da jama’a, yayin da ya godewa gwamnatin Faransa akan taimakawa Afirka da maganin rigakafin cutar korona miliyan 10, wanda tuni aka baiwa Najeriya sama da allura dubu 500.