Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce ya na tunanin komawa gonarsa da ke Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina don ya ci gaba da noma da kiwo Buhari ya yi wannan furucin ne a Istanbul a kasar Turkiyya,
a ofishin jakadancin Najeriya inda aka shirya masa bikin zagayowar shekarunsa A cewar Buhari,
zai yi iyakar kokarinsa wurin bunkasa Najeriya da neman ci gabanta har lokacin da zai mika ragamar mulki a shekarar 2023 ya yi, sannan ya kama gabansa
sar Turkiyya – Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya na da kudirin komawa gonarsa ta Daura, mahaifarsa da ke jihar Katsina, Daily Trust ta ruwaito.
Shugaban kasa ya furta hakan ne a Istanbul, kasar Turkiyya inda aka shirya masa bikin zagayowar ranar haihuwarsa ba tare da saninsa ba a ofishin jakadancin Najeriya da ke kasar.
80.8K Johnny Depp Never Stopped Loving His Mother | Rumour Juice
Buhari ya na kasar Turkiyya yanzu hakan don halartar wani taro inda har ranar haihuwarsa ta zagayo, ya cika shekaru 79 kenan a ranar Juma’a.
An hada cake din da kalolin Najeriya
A cewar kakakin shugaban kasan, Garba Shehu, shugaban kasa ya yanka kek din da aka yi da kalolin Najeriya, kalar kore da fari yayin da ministan harkokin kasar waje, Geoffrey Onyeama ya yi bayani a maimakon sauran ministoci.
A bangaren Buhari kuwa cewa ya yi zai yi wa Najeriya iyakar iyawarsa har ranar da zai sauka daga mulki, sannan ya mika ragamar mulki ga magajinsa sannan ya koma gonarsa don ci gaba da noma da kiwo.