Kungiyar Tintiba ta Arewacin Najeriya da ake kira ACF ta zargi shugaban kasa Muhammadu Buhari da koyawa gwamnonin arewacin kasar nuna halin ko-in-kula dangane da hare haren da ake kaiwa jama’ar yankin ana kashe su a ba tare da nuna wata damuwa ba.
Sanarwar kungiyar wadda ke dauke da sanya hannun Kakakin ta Emmanuel Yawe tace gwamnonin na koyi da halin da shugaban kasa ke nunawa na rashin damuwa da hare haren da ake kai musu da kuma hallaka su.
Yawe yace abinda jama’a ke gani daga shugabannin na nuna cewar sun damu da rayuwar su ce kawai tare da ta iyalan su, amma ba na jama’ar da suke yiwa shugabanci ba.
Sanarwar tace banda Gwamnan Borno Babagana Zulum wanda koda yaushe ke kan hanyar zuwa wajen jama’ar da yake yiwa shugabanci duk lokacin da aka kai musu hari, shugaban kasa Buhari tare da sauran gwamnonin arewacin kasar basu damu da ziyarar wadanda iftila’i ya afka musu ba, ballanta su jajanta musu.
Yawe yace kungiyar ta gabatar da rashin amincewar ta da kuma fushin ta dangane da abinda ta kira amincewa da ci gaba da kashe fararen hula ba tare da kaukautawa ba daga bangaren shugabannin.
Kungiyar tace ko a jiya lahadi ‘Yan bindiga sun hallaka mutane 38 a karmar hukumar Giwa dake Jihar Kaduna, kuma basu ga dalilin da ya hana shugaban kasa Buhari da gwamnan jihar Malam Nasir El Rufai ziyarar inda aka kai harin domin jajanta musu ba.
Yawe ya bada misali akan Gwamna Zulum na Jihar Borno wanda a kwanakin nan ya tashi zuwa Askira Uba domin jajantawa mutanen yankin bayan harin da ya hallaka mutane 10.
Yawe yace mutanen da suke fuskantar wadannan hare hare a yankin arewacin Najeriya sun yanke yakinin cewar babu wanda ya damu da rayuwar su.
Arewacin najeriya dai yana cikin wani mawuyacin hali amma gwamnatin tarayya da gwamnonin jihohin arewa basu ddauki matakin komi ba.