Kakakin majalisar dattijai, Sanata Ahmad Lawal ya bayyana cewaz shugaban kasa, Muhammadu Buhari bai bada umarnin a cire tallafin man fetur ba.
Lawal yace ‘yan Najeriya da yawa sun damu kan maganar cire tallafin man dan hakane ya kaiwa shugaba Buhari kukansu.
Saidai yace shugaban yace bai bada umarnin a cire tallafin man ba. A baya dai ministar kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ta bayyana cewa, nan da tsakiyar shekarar 2022 ne za’a cire tallafin man gaba daya.