Shugaba kasa Muhammadu Buhari ya dawo da maganar zaben ‘dan takaran shugaban kasa da aka yi a APC.
Shugaban na Najeriya mai barin gado ya ce babu dalilin da zai fifita wani daga cikin masu neman takara.
Buhari yana ganin tun da damukaradiyya ta ke aiki, a bar wanda ya iya allonsa ya wanke a jam’iyya.
Shugaba Muhammadu Buhari ya ce da gangan ya ki yarda ya nuna wanda ya ke so a zaben tsaida gwanin shugaban kasa na APC.
Muhammadu Buhari ya nuna babu adalci idan ya ba wani mai neman takara fifiko a tsarin damukaradiyya, The Nation ta kawo wannan rahoto dazu.
Mai girma shugaban na Najeriya ya ce ya nemi shugabancin Najeriya sau uku amma duk ya kare a kotu, don haka ba zai iya daga hannun magajinsa ba.
A zaben fitar da ‘dan takara da jam’iyyar APC ta shirya, shugaban kasar bai yi karfa-karfa ba.
Bai goyi bayan kowa ba
Buhari bai nuna wanda yake sha’awar ya samu takara a APC tsakanin irinsu Bola Tinubu, Yemi Osinbajo, Rotimi Amaechi da kuma Ahmad Lawan ba.
Muhammadu Buhari ya tunawa al’umma yadda Sardaunan Sokoto, Ahmadu Bello ya tabbatar da adalci da gaskiya a lokacin da yake Firimiyan Arewa.
An tuna da Ahmadu Bello
Shugaban kasar ya yi wannan jawabi ne a wajen taron da gwamnatin Nasarawa da gidauniyar Ahmadu Bello suka shirya domin tunawa da Firimiya.
Vanguard ta ce Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Farfesa Ibrahim Gambari ya wakilci Buhari a wajen taron da aka yi garin Lafia a Nasarawa.
A madadin mai gidansa, Ibrahim Gambari ya yi kira ga mutanen Najeriya su karbi sakamakon zabukan da aka yi, ya ce duk masu ta-cewa su tafi kotu.
Wanda aka gayyato domin ya zama mai jawabi shi ne Farfesa Patrick Lumumba daga kasar Kenya, Simon Bako Lalong ma ya tofa albarkacin bakinsa.
Rahoton ya ce taron ya samu halartar tsofaffin Gwamnoni; Babangida Aliyu, Murtala Nyako, Idris Abubakar, Tanko Al-Makura sai Abdullahi Adamu.