A yau ne ake sa ran BoT za tayi zaman da zai dinke barakar Nyesom Wike da Atiku Abubakar.
Ana zargin mutanen Nyesom Wike sun nemi a canza shugaban PDP kafin su bi Atiku Abubakar Bangaren da ke rikici da ‘Dan takaran suna so Atiku ya sa hannu a yarjejeniyar ba zai zarce ba.
Ana sa ran majalisar amintattu na PDP watau BoT za tayi zama domin shawo kan sabanin da ke tsakanin su Nyesom Wike da Atiku Abubakar.
The Guardian za ta iya rahoto cewa tun bayan zaben fitar da gwani ake samun rikici tsakanin ‘dan takaran shugaban kasar da kuma Gwamnan jihar Ribas.
Bayan doke Nyesom Wike da Atiku Abubakar ya yi wajen samun tikitin jam’iyyar PDP, ya dauko Dr. Ifeanyi Okowa ya zama masa abokin takara a 2023.
Da aka zanta da shi, shugaban BoT na jam’iyyar PDP, Sanata Walid Jibrin yace zaman da za su yi a yau Laraba zai tabbatar da an sulhunta bangarorin biyu.
Za a duba bukatun su Wike A wajen wannan taro, jaridar tace za a saurari bukatar da bangaren Nyesom Wike suka gabatar, inda suka nemi a sauke shugaban PDP, Dr. Iyochia Ayu.
Wata majiya daga sakatariyar PDP ta kasa ta shaida cewa mutanen Wike suna so Atiku ya sa hannu a yarjejeniyar wa’adi daya a kujerar shugaban kasa.
Daga cikin bukatun bangaren Gwamnan na Ribas shi ne a ba mutanensa mukamai idan har jam’iyyar PDP tayi nasarar kafa gwamnati a Mayun 2023.
BoT za ta bada shawara A wani jawabi da BoT ta fitar, Jibrin yace za su yi la’akari da duka abubuwan da aka zo da su domin su bada shawara kan matakin da ya kamata a dauka.
Goron gayyatar taron BoT:
“Ina kira ga duka ‘Yan BOT da ke tare da Farfesa Jerry Gana da su halarci zaman BoT na ranar Laraba domin a cin ma matsaya guda.
Bayan wannan taro, za mu hadu da Atiku, Okowa da Wike domin sulhunta matsalar da nufin ganin PDP ta samu nasara da kyau.
” Tun ba yau ba aka fara maganar a sauke Ayu ganin ya fito ne daga Arewacin Najeriya, yankin ‘dan takaran shugaban kasa na zaben 2023, Atiku Abubakar.
A dokar PDP, NEC ce kurum za ta iya tunbuke shugaban jam’iyya, sai kuma idan an gudanar da babban zaben shugabanni na kasa kamar yadda aka yi a 2021.
Rikicin PDP kadan ne a kan na APC Sanata Jibrin yake cewa rikicin cikin gidan da ake samu a PDP, bai kai rigimar da jam’iyyar APC ta samu kanta a dalilin tikitin Musulmi da Musulmi ba.
An ji labari Shugaban Gwamnonin Arewa ake sa ran za a sanar a matsayin Darekta Janar da zai jagoranci APC a yakin neman Shugaban kasa na 2023.
Source:hausalegitng