Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar All Progressives Congress APC, ya taka rawa a wurin kaddamar da yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyarsa a Jos.
Dandazon masoya da magoya bayan mai fatan zama shugaban kasar sun masa maraba ta girma yayin da ya iso filin wasanni na Rwang Pam tare da abokin takarar sa.
Bisa irin tarba da maraba da dandazon mutanen suka masa, Bola Tinubu ya taka rawa yayin da sautin waka ke tashi a wurin taron.
Jam’iyyar All Progressives Congress, APC, ta kaddamar da yakin neman zabenta a Jos, babban birnin jihar Plateau, a ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba.
Bola Tinubu, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar mai mulki da abokin takararsa, Kashim Shettima, sun isa filin motsa jiki na Rwang Pam kafin zuwar Shugaba Muhammadu Buhari.
Bisa alamu mai fatan zama shugaban kasar ya ji dadin irin tarbar da magoya bayansa suka masa yayin da ya iso.
Abin da ke faruwa da kamfen din takarar shugaban kasa na APC, Bola Tinubu, Remi Tinubu Tsohon gwamnan na jihar Legas ya nuna bajintarsa na rawa a wani bidiyo da shafin Tinubu/Shettima Media Support ta wallafa a Tuwita.
Tawagar watsa labaran ta yi wa bidiyoyin lakabi da: “Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, dan takarar mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima sun iso filin wasanni na Rwang Pam don kaddamar da kamfenin din APC.”
Dan takarar shugaban kasar mai shekara 70 ya yi wani motsi da hannunsa da yatsunsa yayin da ya ke taka rawa ga wakar da ake yi a wurin.
A wani rahoto, Simon Lalong, gwamnan Filato, ya ayyana ranar Talata, 15 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu a dukkan jihar saboda ziyarar Shugaba Muhammadu Buhari, Bola Tinubu da wasu shugabannin jam’iyyar APC.
Hakan na cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun kwamishinan labarai na jihar, Dan Manjang, da aka fitar a ranar Litinin 14 ga watan Nuwamba.
Source:LEGITHAUSA