Miyagun mayakan ta’addanci na Boko Haram sun kai mummunan farmaki kauyen Kilangal da ke karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno.
‘Yan ta’addan an gano sun halaka wasu mutane masu tarin yawa sannan wasu sun jigata yayin da suka banka wa wasu gidaje wuta Bayan sa’o’i biyu, jiragen yakin sojin saman Najeriya sun bayyana domin kai dauki, amma tuni ‘yan ta’addan suka gama barnarsu tare da komawa daji.
Akwai yuwuwar mutane masu tarin yawa sun rasa rayukansu yayin da wasu suka samu raunika yayin da mayakan ta’addancin Boko Haram suka kai farmaki karamar hukumar Askira Uba a jihar Borno.
Daily Trust ta ruwaito cewa, ‘yan ta’addan suna dira kauyen Kilangal, asalin garin su Injiniya Abdullahi Musa Askira, mataimakin kakakin majalisar jihar Borno a ranar Lahadi, kuma sun banka wa gidaje wuta.
A wani labarin na daban ‘Yan sanda a kasar Faransa sun ce akalla mutane sama da 50 aka kama a karshen mako lokacin da magoya bayan kasar Algeria suka gudanar da murnar nasarar da kasar ta samu wajen lashe kofin kwallon kafar kasashen Larabawa, kuma akasarin su an kama su ne kusa da fadar shugaban kasa.
Algeriya ta doke Tunisia da ci 2-0 a wasan karshe da aka kara a Qatar wajen lashe kofin, abinda ya sa magoya bayan kasar a biranen Faransa da suka hada da Paris da Lyon da kuma Roubaix suka fantsama tituna domin nuna murnar su.
Kasa da makonni uku kenan da Ministan harkokin wajen Faransa Jean-Yves Le Drian ya isa Algeria a wani yunkuri na gyara alakar kasashen biyu bayan sabanin da suka samu a baya-bayan nan wanda ya kai ga musayar janye jakadun juna.