Gwamnatin Birtaniya a yau lahadi ta sanar da daukar wasu jerryn matakai da nufin takaita yaduwar sabon nau’in cutar Omicron .
Daga cikin wadanan matakai da gwamnatin kasar ke sa ran za su fara aiki nan da ranar talatar makon gobe,sun hada da tilastawa jama’a amfani da kyalen rufe hanci da baki da kuma tsaurara matakan shiga kasar ta Birtaniya daga baki.
Ministan kiwon lafiyar kasar Sajid Javid ya sheidawa wata kafar neman labarai cewa ya zama tilas jama’a su koma amfani da kyalen rufe hanci da baki a cikin motocin sufuri da gidajen cin abinci da shaguna daga ranar talata.
Birtaniya ta ce a shirye take ta shirya tattaunawa da wasu kasashe dangane da batun da ya shafi yan cin rani da masu tsallakawa da su a yankin la Manche.
Ministan harakokin cikin gidan kasar Priti Patel ta ce ba zata halarci taron dake gudana a wannan lokaci tsakanin kasashen Jamus, Netherlands, Faransa da Belgium, taron da zai tattauna dangane da batun yan cin rani a yankin Calais dake arewacin Faransa.
A maimakon haka, Ministar ta bayyana cewa nan gaba Birtaniya na kyautata zaton shirya wani taro na ta daban ,inda take sa ran samu tattaunawa da wakilan kasashen Turai nan da makon sama.