Gwamnatin Birtaniya ta sauya matsayinta a kan kungiyar nan mai fafutukar neman kasar Biafra wato IPOB, tana mai amincewa da saka ta a jerin kungiyoyin ‘yan ta’adda da gwamnatin Najeriya ta yi.
A daftarin manufarta ta bayar da mafaka da ta sabanta a watan Mayun nan, gwamnatin Birtaniya ta cire ‘yayan kungiyar IPOB daga cikin masu neman mafaka a Ingila.
A cikin watan Afrilun shekarar 2021 ne rahotanni suka bayyana a kafafen yada labarai cewa, Birtaniya na shirin bada mafaka ga ‘yayan kungiyar ‘yan awaren IPOB da ake musguna wa, a matsayin wani bangare na manufofinta a kan ‘yan gudun hijira da ta walllafa a lokacin.
Amma ‘yan kwanaki bayan wallafa daftarin, gwammanti Birtaniya ta soke shi, biyo bayan korafi daga takwararta ta Najeriya.
A cikin daftarin manufofin nata, gwamnatin Birtaniya ta bayyana IPOB a matsayin kungiyar ‘yan ta’adda, wadda za ta cire ta daga shirinta na bada mafaka, sakamakon hannu da take da shi a kashe kashe da tashin hankali a yankin kudu maso gabashin Najeriya
Daftarin manufofin ya kuma ce, duk wanda aka cire daga jerin wadanda suka cancanci mafaka, tabbaci hakika ba ya cikin wadanda za su samu kariya ta jinkai.
‘Ya bindiga da ake zaton ‘yayan kungiyar IPOB ne, sun tsananta aikata ta’asa a yankin kudu maso gabashin Najeriya a baya bayan nan.
A wani labarin na daban Rundunar sojin Burkina Faso ta ce dakarunta bakwai da kuma wasu ‘yan sa-kai hudu sun rasa rayukansu, yayin harin kwanton bauna har kashi biyu da ‘yan ta’adda suka kai musu a yankin arewacin kasar mai fama da matsalar tsaro.
Sanarwar da rundunar sojin Burkina Fason ta fitar a wannan Juma’a ta ce, an kai harin farko ne a kusa da garin Solle ranar Alhamis din da ta gabata inda sojoji biyu suka mutu da wasu farar hula hudu, ‘yan sa-kai da ke taimaka wa sojojin.
A wani harin na dabam kuma, dakaru biyar ne suka halaka a dai ranar ta Alhamis a garin Ouanobe.
Sanarwar ta kara da cewa, mutane 9 ne suka jikkata, yayin da kuma aka gano gawarwakin maharan kimanin 20 lokacin da jami’an tsaro ke sintiri a wuraren da aka kai farmaki, bayan da suka tarwatsa ‘yan ta’adddan, tare da lalata makamansu da dama da kuma kwace wasu.
Tun daga shekarar 2015, kungiyoyin da ke da alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS ke kai hare-hare a arewaci da gabashin Burkina Faso, inda suka kashe mutane sama da 2,000 tare da raba kusan miliyan biyu da muhallansu, tashin hankalin da ya shafi sassan Mali da Nijar da ke makwabtaka da kasar.