Sojan dake mulki a kasar Guinea-Bissau sun tabbatar da shawo kan yunkurin juyin mulkin da aka samu Talata kuma rayukan mutane 11 suka salwanta sakamakon yunkurin kuma suna binciken dalilin faruwar hakan.
A ranar Talata data gabata wasu sojoji dauke da manyan bindigogi suka zagaye gidan gwamnati dake Bissau inda Shugaban kasar da kuma Firaminista ke taro.
Shugaba Embalo mai shekaru 49 ya shaidawa manema labarai cewa ya yi katarin tsallake rijiya da baya, bayan kwashe sao’i biyar ana ta barin wuta da niyyar kwace gwamnati.
Binciken majiyoyin soja dake Guinea-Bissau sun shaidawa kamfanin Dillancin Labaran Faransa AFP cewa sau hudu ana yunkurin juyin mulki tun bayan samun ‘yanci daga Portugal a shekara ta 1974.
A yanzu haka hukumomin kasar sun kaddamar da cikakken binciken yumkurin juyin aikin.
A wani labarin na daban kuma Tawagar kwallon kafa ta Super Eagles doke Guinea Bissau a gasar cin kofin Afrika da Kamaru ke karbar bakwanci da ci 2 da nema.
A ranar alhamis 20 ga wannan wata na Janairu, Aljeriya zata ketse reni da Cote D’Ivoire a rukunni na biyar, Saliho a na ta geffen za ta kara da Guinee Equatorial.