Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bayyana kwarin guiwarsa cewa nan ba da jimawa ba.
PDP zata lalubo bakin zaren ta dinke ɓarakarta Har yanzun dai ana kai ruwa rana tsakanin tsagin G5 da ya kunshi gwamnonin PDP biyar da shugabancin jam’iyya na kasa.
Wasu bayanai sun ce Iyorchia Ayu ya yi alkawarin zai sauka idan har ɗan arewa ya lashe tikitin takarar shugaban kasa.
Gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya tabbatar da cewa batutuwan da suka raba jam’iyyar PDP ta ƙasa, nan ba da jimawa ba za’a warware su.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa Gwamnan ya bayyana haka ne a wurin taron masu ruwa da tsaki wanda ya gudana a gidan gwamnatinsa dake Makurɗi.
Ortom, mamba a tawagar gaskiya da ake wa laƙabi da G5, ya yi ikirarin cewa ɓangarorin biyu masu takun saka da juna sun fara kokarin shawo kan matsalolin da suka raba su.
Legit.ng Hausa ta tattaro cewa shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Dakta Iyorchia Ayu, ya jima ba su ga maciji da gwamnonin jam’iyar na tsagin G5.
Gwamnonin sun haɗa da Nyesom Wike na jihar Ribas, Seyi Makinde na jihar Oyo, Okezie Ikpeazu na Abiya, Ifeanyi Ugwuanyi na Enugu da Ortom na Benue.
Tawagar gwamnonin sun nemi Ayu ya yi murabus daga kujerarsa a maye gurbin da ɗan kudu domin dai-daito da adalci tsakanin arewa da kudancin Najeriya.
Shin PDP ta kama hanyar warware rikicin?
Amma gwamna Ortom, a wurin taron ya bayyana yakininsa cewa zaman lalubo hanyar sulhu da ake ci gaba da yi zai haifar da ɗa mai ido.
“Mun shirya tsaf domin tabbatar da PDP ta samu nasara a zaɓe, batutuwan da suka raba kawunan mu, nan ba da jimawa ba zamu warware su.”
Gwamnonin G5: Wasu gwamnonin PDP Na Shirin Komawa APC?
Gaskiya Ta Bayyana “Akwai matsaloli da dama a matakin ƙasa amma mun yi amanna cewa da ikon Allah zamu shawo kansu komai ya zama tarihi.”
A wani labarin kuma Na fara kishin-kishin kan ɗan takarar shugaban ƙasan da gwamna Wike zai goya wa baya a 2023.
Jita-jita ta fara yawaita kan cewa da yuwuwar Wike da sauran ‘yan tawagarsa su haɗa ƙawance da Bola Ahmed Tinubu na APC bayan raba gari da Atiku.