Gabanin zaben 2023, dan takarar kujerar shugaban kasan Peoples Democratic Party (PDP) ya roki al’ummar Benue.
A jihar Benue, ya roki al’ummar su daina yi masa kallon Fulani, amma halastaccen dan Najeriya.
Ya bayyana cewa gwamnatinsa zata dama da kowa, Musulmi ko Kirista kuma za’a girmama doka.
Dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Atiku Abubakar, ya bayyana muradunsa ga al’ummar jihar Benue.
Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, wanda ya bayyana hakan ranar Alhamis, 17 ga Nuwamba a taron cocin 82nd Synod of the Universal Reformed Christian Church, aka NKST, a Mkar, jihar Benue ya ce zai cigaba da kasancewa tare da al’ummar Benue kamar yadda yayi a baya.
Atiku wanda ya samu wakilcin Farfesa Iorwuese Hagher da Hanarabul Chille Igbawua na kwamitin kamfen PDP, yace:
“Jam’iyyata PDP mai hankali ce ga rabon mulki tsakanin Kiristoci da Musulmai a kasar nan.”
“Wadanda suka ki girmama addininmu sun yi hakan ne da gayya. Ba zamu bari su tsira ba.”
Atiku Yace al’ummar Benue su zabesa Atiku ya yi kira da jama’ar Benue su daina yi masa kallon Fulani amma a matsayinsa na Atiku Abubakar.
Kamar yadda Vanguard ta ruwaito, ya yi waiwaye kan rawar da ya taka lokacin rikicin Zaki-Biam da Gbeji da Adoor kuma yadda ya tsaya da al’ummar Benue.
Yace: “Mun shiga lungu da sakon Zaki-Biam ranar da abin ya faru, mun yi Alla-wadai da kisan al’ummar Tibi kuma an ga gaskiyarmu daga baya lokacin Soji suka bada hakuri.”
“Har yanzu ni ne Zege Mule u Tiv, ina tabbatar muku cewa idan kuka zabeni matsayin Shugaban kasa, babu dan Najeriyan da zai gaza bacci saboda yan ta’adda.”
A wani labarin kuwa, yan Jam’iyyar adawa ta PDP a jihar Plateau sun yiwa Alhaji Atiku Abubakar alkawarin kawo masa kuri’u miliyan biyu a zaben 2023.
Source:Legithausa