Majalisar dokokin jihar Zamfara ta zabi Sanata Muhammad Hassan Nasiha a matsayin sabon mataimakin gwamnan jihar da ke Arewa maso Yamma bayan tsige Barista Mahdi Gusau, inji rahoton Channels Tv.
A zaman da aka yi yau, kakakin majalisar, Nasiru Mua’zu, ya karanta wasikar da gwamnan jihar Bello Matawalle ya aike masa na zabar Sanata Muhammad a matsayin mataimakin gwamnan jihar Zamfara.
An zabi Hassan ne sa’o’i bayan tsige Mahdi Gusau a yau Laraba. Sanata Hassan yana wakiltar mazabar Zamfara ta tsakiya.
Dalilin zaban sabon mataimakin gwamna An tsige tsohon mataimakin gwamna Gusau ne bayan da majalisar ta karbi rahoton kwamitin da babban alkalin jihar, Mai shari’a Kulu Aliyu ya kafa.
Dama a baya an kafa kwamitin binciken zargin da ake yiwa mataimakin gwamnan.
Kwamitin mai mutane bakwai karkashin mai shari’a Halidu Soba mai ritaya ya mika rahotonsa majalisar dokokin jihar ne da ke Gusau babban birnin jihar.
A cewar wani mamba a kwamitin Oladipo Okpeseyi, kwamitin ya gudanar da aikinsa bisa gaskiya. Kwamitin ya fara zamansa ne a ranar litinin kuma ya kammala zaman washegari.
Amma Gusau wanda ake bincika bai halarci zaman binciken ba. Wasu daga cikin zarge-zargen da ake masa sun hada da saba wa Kundin Tsarin Mulki, da rashin da’a, da zamba, da kuma cin zarafin mukaminsa. Karin bayani na nan tafe..