Jaridar Daily Trust da ake wallafawa a Najeriya tace bata garin sun yiwa jami’an ‘Yan Sandan kwantar bauna ne, inda bayan sun harbe su, suka kuma kona su a cikin motar su kirar Toyota Sienna.
Shaidar gani da ido ya bayyana cewar an kona gawarwakin jami’an yadda ba a iya gane , kuma kakakin rundunar ‘Yan Sandan Jihar Delta Bright Edafe ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Jami’an ‘Yan Sanda da soji na fuskantar irin wadannan hare haren a yankin kudu maso gabashin Najeriya wanda ake zargin ‘yayan kungiyar IPOB dake fafutukar kafa kasar Biafra.
Akalla jami’an Y’an Sanda sama da 150 aka kashe a wannan yankin a cikin wannan shekara tare da sace wasu makaman su.
A wani labarin na daban ‘Yan bindiga a Najeriya yau sun sake kai hari Karamar hukumar Shinkafi dake Jihar Zamfara, inda suka yi artabu da mutanen garin, kafin daga bisani a tura jami’an tsaro.
Daya daga cikin shugabannin garin Suleiman Shuaibu Shinkafi ya shaidawa RFI Hausa cewar anyi artabu sosai tsakanin mazauna Shinkafi da ‘Yan bindigar kafin zuwan tawagar sojoji da ‘Yan sanda abinda ya sa barayin suka gaggauta janyewa daga garin.
Shinkafi yace mazauna garin sun yi nasarar kashe daya daga cikin ‘Yan bindigar kafin janyewar su, yayin da suma suka harbi mazaunin garin guda.
Jihar Zamfara na ci gaba da fuskantar hare haren ’Yan bindiga dake sace shannu da mutane, tare da hallaka jama’a ba tare da kaukautawa ba.
Wannan ya sa Gwamna Matawalle rufe daukacin makarantun jihar da hana cin kasuwannin mako-mako da saka dokar hana fitar dare da kuma hana sayar da man fetur da yawa ga jama’a, matakin da ya girgiza ‘Yan bindigar.