Da alama dai tsugunno bata karewa kungiyar Barcelona ba musamman a kakar wasa ta bana, inda a yanzu haka ta fara neman kulla yarjejeniya da wasu ‘yan wasa guda biyu, domin cike gurbin da dan wasanta na gaba Sergio Aguero ya bari.
Dan wasan na Argentina da ya koma taka leda a Barcelona, na tsaka da buga wasansa na shida a kungiyar ne inda suke karawa da Alaves a gasar La Liga sai ya fara fama da ciwon kirji, a karshen makon da ya gabata.
A halin yanzu ‘yan wasan da Barcelona ke neman kulla kwatiragi da su domin cike mata gurbin Aguero sun hada da Raheem Sterling na Manchester City da kuma Dani Olmo na kungiyar RB Leipzig.
A wani labarin na daban mai kama da wannan kuma kungiyar kwallon kafa ta Barcelona ta gaza lashe wasan ta na farko bayan korar manaja Ronald Koeman, sakamakon karawar da ta yi da kungiyar Celto Vigo yau asabar wanda aka tashi 3-3.
Fati Vieira ya fara jefawa Barcelona kwallon ta na farko a minti 5 da fara wasa, kafin Busquets ya jefa ta biyu a minti 18, sannan Depay ya jefa ta 3 a minti 34.
Dawowa daga hutun rabin lokaci Iago Aspas ya farkewa Celta Vigo kwallon ta na farko a minti 52, Nolito ya farke na biyu a minti 74, yayin da Aspas ya jefa kwallon sa ta 2 wadda itace ta 3 da Celta Vigo taci a wasan a minti 96.
Wannan ba karamar nasara bace ga Celta wadda ke matsayi na 15 a tebur kafin fara wasan, yayin ta zaam koma baya ga Barcelona wadda a wannan lokaci ke matsayi na 9 a teburin La Liga da maki 17.