Da alama dai tsugunno bata karewa kungiyar Barcelona ba musamman a kakar wasa ta bana, inda a yanzu haka ta fara neman kulla yarjejeniya da wasu ‘yan wasa guda biyu, domin cike gurbin da dan wasanta na gaba Sergio Aguero ya bari.
Dan wasan na Argentina da ya koma taka leda a Barcelona, na tsaka da buga wasansa na shida a kungiyar ne inda suke karawa da Alaves a gasar La Liga sai ya fara fama da ciwon kirji, a karshen makon da ya gabata.
A halin yanzu ‘yan wasan da Barcelona ke neman kulla kwatiragi da su domin cike mata gurbin Aguero sun hada da Raheem Sterling na Manchester City da kuma Dani Olmo na kungiyar RB Leipzig.
A wani labarin nna daban Barcelona za ta fara rayuwa ba tare da kocinta Roland Koeman da ta sallama ba a fafatawa tsakaninta da Alaves a ranar Asabar, inda take sa ran rage tazarar da aka ba ta a gasar La Ligar Spain, tare da maido da karsashinta gabanin wasan gasar zakarun nahiyar Turai da za ta gwabza da Dynamo Kiev.
Rahotannin sun bayyana cewa Xavi Hernandez yana daf da kama aiki a matsayin mai horarwa a Camp Nou, kungiyar da ta dauke shi a matsayin dan wasa tun yana dan shekara 11, suka kuma yi hannun riga a shekarar 2015, sai dai babu tabbas ko hakan zai yiwu kafin karshen mako.
Barcelona ta samu nasar sau 2 ne kawai a wasanni 7 da ta buga a La Liga, lamarin da ya sa yanzu take matsayi na 9 a teburin gasar, kuma Real Betis da ke matsayi na 4 ta ba ta ratar maki 6.