Hukumar zabe mai kanta ta kasa ta bayyana cewa banka wa ofisoshin su wuta da ake ci gaba da yi wa ofisoshinta makirci ne da wasu maciya amanar kasa ke kullawa.
Kwamishinan hukumar kuma shugaban kwamitin yada labarai da ilimantar da masu zabe, Festus Okoye, ya bayyana haka yayin da yake nuna damuwar hukumar kan abin da ke faruwa na banka wa ofisoshin wuta bayan wani taron gaggawa a Abuja ranar Litinin.
An gudanar da taron ne sa’o’i bayan da wasu ‘yan bindiga suka kutsa kai cikin babban ofishinta da ke Awka, babban birnin jihar Anambara, wanda aka kone kurmus bayan wani artabu da suka yi da jami’an tsaro.
A cikin wata sanarwa, Okoye ya ce ofishin hukumar a karamar hukumar Igboeze ta Kudu ta jihar Enugu ma an barnata shi.
Sanarwar ta kara da cewa, “Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta kasa (INEC) ta yi zaman gaggawa a yau, Litinin 24 ga Mayu 2021, yayin da ake ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyinta a wasu jihohin Tarayyar ba tare da wata turjiya ba.
“A cikin abubuwan da suka faru na baya-bayan nan, an kai wa ofisoshi uku na hukumar hari a jihohin Anambra, Imo da Enugu. Kwamishinan Zabe (REC) na Jihar Anambra, Dokta Nkwachukwu Orji; da takwaransa na jihar Imo, Farfesa Francis Ezeonu, da na jihar Enugu, Emeka Ononamadu, sun ruwaito cewa an kai hare-haren ne a lokuta daban-daban a daren Lahadi, 23 ga Mayu 2021. ”
Okoye ya bayyana harin na Anambra a matsayin babban koma-baya ga shirye-shiryen zaben gwamna da aka shirya a ranar 6 ga Nuwamba a jihar.
Ya ce, “Ofishin da ke zaman Hedikwatar Jiha na hukumar da ke Awka an banka masa wuta inda aka yi mummunan barna a wasu cibiyoyin hukumar kawo yanzu.
“Cikin tsari maharan suke kai hari a wuraren da suke so. An Banka wa Cibiyar tattara kuri’u yayin manyan zabuka wuta.
Abin da ya kawo mana cikas ga shirye-shiryenmu na zaben gwamna da aka shirya yi a ranar 6 ga Nuwambar 2021, ofisoshi biyu da ke dauke da kayayyakin zaben sun kone.
“Akwai injunan samar da wutar lantarki 376 ga dukkan mazabun zabe da kuma karin wasu kayan aiki sun kone kurmus. Kwanan baya an canza masu samar da wutar lantarki daga kananan hukumomi zuwa shalkwatarmu bisa la’akari da cewa ya fi ofisoshin kananan hukumomi tsaro.
“Haka nan, a matsayin wani bangare na matakan da hukumar ta dauka don tabbatar da nasarar zaben gwamna a karshen wannan shekarar, kusan kashi 50% na kayan aikin da ba na sirri ba ne sosai da ake bukata don zaben gwamna na ranar 6 ga Nuwambar 20201 da aka riga aka kai jihar an yi asararsu a wutar. Bugu da kari, motocin amfani guda bakwai (Toyota Hilud) duk sun kone.
“Har ila yau a jiya (Lahadi), an kai wa ofishinmu da ke karamar hukumar Ahiazu Mbaise hari da misalin karfe 6.45 na yamma hari inda aka cinna wuta. Abin farin ciki, ba duka kayan da ke ofishin ne aka yi asararsu ba.
“Da misalin karfe 1.00 na daren jiya (Lahadi), aka sake kai hari ofishinmu na karamar hukumar Igboeze ta Kudu. Ofishin ya kone kurmus gabanin Kashe Gobara ta Jihar Enugu su kawo dauki da tare da hana wutar da ta tashi fantsama zuwa wasu sassa na ginin.
“Wannan shi ne hari na uku da aka kai wa cibiyoyin INEC a cikin jihar cikin kasa da makonni biyu bayan lalata ofishin mu na karamar hukumar Udenu a ranar 13 ga Mayu 2021 da kuma ginin Hedikwatar Jiha da ke Enugu a ranar 16 ga Mayu 2021.
“Dukkanin abubuwan uku da suka faru a Anambra, Imo da Enugu an sanar da da ‘yan sanda don gudanar da bincike.
“Duk da cewa ba a rasa rayukan mutane ba, wadannan a bayyane suke makirce-makirce ne ake kullawa da nufin kawo nakasu ga Hukumar wajen gudanar da ayyukan zabe, musamman a jihar Anambra.
“Hare-hare kan cibiyoyin Hukumar yanzu sun zama lamarin gaggawa na kasa. A kan haka, Hukumar za ta yi wa gwamnati da masu ruwa da tsaki bayani game da wadannan abubuwa.
“Duk da wadannan matsalolin, Hukumar ta kuduri aniyar ci gaba da sauke nauyin da ke kanta ciki har da gudanar da zaben gwamnan na Anambra da aka shirya,” in ji sanarwar ta.