Gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad ya sha rantsuwar kama aiki a matsayin gwamnan Jihar Bauchi karo na biyu bayan samun nasarar da ya yi a zaben gwamna da aka gudanar a 2023.
An gudanar da bikin rantsuwar ne a filin wasanni na Stadium da ke Bauchi ranar Litinin.
Babbar Alkalin Alkalan jihar Bauchi, Mai Shari’a Rabi Talatu Umar ce ta rantsar da Gwamna Bala da mataimakinsa , Hon. Mohammed Auwal Jatau lamarin da yanzu ya nuna cewa su ne sabbin jagororin jihar Bauchi bayan samun nasara da suka yi a karkashin jam’iyyar PDP.
Sabon mataimakin Gwamnan Jihar Bauchi Auwal Jatau ya amshi rantsuwar kama aiki ne da karfe 12:29pm, yayin da gwamnan Bala Muhammad Kuma da ya samu rakiyar matarsa, Aisha ya amshi rantsuwar da karfe 12:53pm.
Kafin a rantsar da Balan ya amshi faretin ban girma daga wajen jami’an ‘yansansan Nijeriya, a babban taron rantsar da gwamnan manya da kananan Sarakunan gargajiya na jihar sun halarta tare da ‘yan siyasa da masu ruwa da tsaki na jihar. An samu halartar dandazon jama’a a wajen bikin.
Bala da Katau, kafin rantsar da su, an karanto cikakken tarihinsu a bainar jama’a daga haihuwarsu, ayyukansu, mukaman da suka rike da gwagwarmayarsu a siyasance har zuwa yau.