Dan Majalissar da yayi irin wannan ikirarin a kwanakin baya yace ba yayi bane dan wata manufa sai dan motsa yan jam’iyya.
Sai gashi a wannan karon ma dai ya kuma inda ya zagi duk wanda baya goyan bayansu musamman ma a akwatin zabe.
Alhassan yayi kaurin suna wajen fitar da irin wadannn maganganun da kuma wasu abubuwa wanda a zahiri suna nufin tarzoma.
Bayan ziyarar da dan takarar shugaban Kasa na jam’iyyar APC yayi a jihar kano, an jiyo bulaliyar majalissar wakilai na wani ikirari game da masu zabe.
A wani bidiyo da dan jaridar nan mai binciken kwakwaf ya wallafa a shafinsa na facebook, an jiyo Doguwan na zagi da cin mutunci ga duk wanda ba jefa musu kuri’a ba a lokacin da yaje zabe a akwati.
“Wallahi ku indan baza ku iya ba, to wallahi mu zamu iya, ba wanda zai zo akwati yace bai mana wani abu sai munci ubansa, kai ba ubansa ba ma sai munci uban-ubansa, ko kuma wani mutum yace ma ka zabi kwankwaso”
Doguwan na maida martani ne ga wanda suke cewa a ranar zabe zasu je har akwatin doguwan su kada shi.
Yan Siyasa a Nigeria na takama da nasarar da suka samu a kwatin da suke kada kuri’a a matsayin wani abu da zasu yi alfahari dashi.
Waye Doguwa Alhassan Ado
Doguwa shine dan majalissar Doguwa da Tudun-Wada a zauren majalissar wakilai ta kasa, kuma ya shafe sama da shekara 20 a majalissar yana wakiltar wannan mazabun nasa.
Ya fara ne tun daga shekarar 1999 har zuwa yanzu da ake zaman majalissa ta tara a zauren, kuma ya rike mukamai da dama da suka hada da mataimakin shugaban masu rinjaye, shugaban kwamituttuka da kuma yanzu yake a matsayin bulaliyar majalissa wato mai ladabtarwa.
A kwanakin baya Alhassan Ado Doguwa yayi rin wannan ikirarin na cewa: “Kodai mutum ya zabo jam’iyyar APC ko kuma ya ci ubansa”
To sai dai Doguwan yayin da yake zantawa da manema labarai ya ce shi bai fadi haka da zummar tayar da zaune tsaye ba.
A’a ya fadi hakan ne da zummar motsa mabiya jam’iyyar da samu musu karsashi.
Source:LegitHausa