Fira Ministan Australia Scott Morrison, ya kaddamar da asusun saka hannun jari na dalar Australia biliyan 738 don hanzarta fara aiwatar da sabbin fasahohin rage fitar da hayaki mai guba, da kuma fara adana iskar ta carbon, domin gwamnatinsa ta cimma muradun yaki da matsalar dumamar yanayi.
Bayan kaddamar da gidauniyar, Morrison ya bayyana fatan kamfanoni masu zaman kansu su ba da tasu gudunmawar da za ta kai akalla dalar Australia miliyan 500 ga asusun.
Sabuwar manufar gwamnatin Australia ta neman rage hayakin Carbon da ake fitarwa a kasar ya zo ne bayan da Fira Minista Morrison ya sha suka sosai a taron Majalisar Dinkin Duniya kan sauyin yanayi a birnin Glasgow dake Scotland, saboda gazawar da ya yi wajen tsara cimma muradun rage matsalar sauyin yanayi nan da shekarar 2030.
A halin yanzu dai Autralia na da burin rage fitar da hayaki da kashi 26 ta yadda zai koma zuwa kashi 28 cikin 100, a kasa da matakin da ta rika fitarwa a shekarar 2005.
A wani labarin na daban wararru sun yi gargadin cewa shiga taron sauyin yanayi na Duniya a Glasgow, cike da burin a yi ko mutu, don takaita dumamar yanayi zuwa maki 1.5 a ma’aunin Celsius, ba shi ne abin damuwa ba.
Daraktan Cibiyar Kula da Tsarin wanzuwar lamurran yanayi da muhalli na Duniya a Jami’ar Exeter dake Ingila Tim Lenton, ya ce babban abinda ke hana masana kimiyya barci a halin yanzu shi ne fargabar yadda ayyukan dan adam ka iya haddasa dumamar yanayi kaiwa makura abinda zai janyo barkewar bala’o’I babu kakkautawa.
Wadannan bala’o’in kuwa sun hada da narkewar dubban tsaunukan kankarar dake yankunan Greenland da yammacin Antarctica, abinda ko shakkah babu zai haddasa tumbatsar tekuna ta yadda tudunsu zai karu da fiye da mitoci goma sha biyu kwatankwacin kafa 40 kenan.
Masanan sun kara da gargadin cewa muddin dan adam bai daina bulbalar da sinadarai masu cutar da yanayi ba, to fa dumamar iska ko yanayin zai kone Amazon wanda shi ne daji mai surkukin itatuwa mafi girma a duniya, wanda kuma dan adam ya dogara da shi don shanye gurbatacciyar iskar carbon, kana ya samar masa iskar Oxygene, kamar yadda aka tabbatar a kimiyyance.
Wata boyayyar barazana kuma da duniyar mu a yau ke fuskanta sakamakon dumamar yanayi ita ce karewar wani nau’in kasa mara zurfi mai suna Permafrost, da galibi ake samunta a yankin Siberia dake Rasha. Kasar ta Permafrost dai na rike ne da ninki biyu na adadin iskar gas mai guba da tuni ta kwarara cikin Atmosphere, wato jakar Iskar dake zagaye da duniyar da muke ciki.