An sahale wa dan wasan gaba na Arsenal Pierre Emerick Aubameyang da ya fice daga tawagar Gabon da ke fafatawa a gasar cin kofin Afrika a Kamaru sakamakon fama da cutar Korona.
Kazalika Gabon ta mayar da dan wasanta na tsakiya Mario Lemina zuwa kungiyarsa ta Nice da ke Faransa, bayan dan wasa ya gaza buga ko da minti guda a wasanni guda biyu da kasarsa ta yi da Comoros da Ghana a gasar ta cin kofin Afrika.
Shi ma dai Lemina na fama ne da cutar Korona, abin da ya hana shi haskawa a gasar ta Afrika.
A wani labarin na daban Tawagar Equatorial Guinea ta lallasa Algeria da kwallo 1 mai ban haushi a karawarsu ta jiya, nasarar da ta bar Algeriar mai rike da kambun gasar cike da fargabar yiwuwar iya ficewa daga gasar ta cin kofin Afrika tun daga matakin rukuni.
Har zuwa yanzu Algeria mai rike da kambun na gasar cin kofin Afrika na da maki 1 ne tal bayan tashi wasanta na farko babu kwallo tsakaninta da Sierra Leone, kuma matukar ta na bukatar tsallakewa zuwa mataki na gaba, dole ne ta yi nasara kan Ivory Coast.
Nasarar ta Equatorial Guinea kan Algeria ya kawo karshen wasanni 35 da kasar ta arewacin Afrika ta doka ba tare da anyi nasara akanta ba, wato dai shi ne shan kayen tawagar na farko tun bayan watan Oktoban 2018.