Fiye da attajiran Duniya 100 ne suka mika bukatar ganin gwamnatoci na karbar haraji a hannunsu fiye da kowa dai dai lokacin da wani rahoto ke ganin harajin attajiran duniya na dala tiriliyan 2.52 a shekara guda zai taimaka wajen wadata Duniya da alluran rigakafin corona.
Cikin wata budaddiyar wasika da attajirai 102 suka aikewa taron taron tattalin arziki na Davos wanda ke gudana ta bidiyon intanet sun bayyana damuwa kan yadda tsarin karbar harajin da ake amfani da shi a yanzu ya ke kara arzurta attajirai.
Wasikar wadda attijarai suka yiwa lakabi da ‘‘Ku karbi haraji daga garemu attajirai yanzu’’ ta isa ga taron na Davos ne a dai dai lokacin da rahoton Oxfam ke nuna yadda za a iya tattara haraji daga hannun attajiran duniya da yawansa ya kai dala tiriliyan 2 da biliyan 52 a shekara guda wanda zai iya wadata duniya da alluran rigakafin corona baya ga cire mutane biliyan 2 da miliyan 300 daga talauci.
Wasikar ta ce wajibi ne kassahen Duniya su yi adalci wajen karbar haraji daga hannun attijarai yadda yakamata sabanin tsarin da ake amfani da shi wajen kara arzurta mawadata da kuma talauta talakawa.
Attajiran sun mika wannan wasika ne kwanaki biyu bayan wani rahoton kungiyar Oxfam ya sanar da yadda attajiran Duniya 10 suka rubanya arzikinsu a lokacin annobar corona da dala tiriliyan 1 da rabi karon farko da aka ga irinsa a shekaru 2.
Wasikar attajiran ta ci gaba da cewa, la’akari da halin da corona ta jefa duniya, wajibi su bayar da haraji fiye da yadda suke bayarwa a baya don ceto miliyoyin rayukan da ke fuskantar barazana.
Attajiran da ke da hannu a wasikar neman karin harajin akansu sun kunshi wasu daga Amurka da Canada da Jamus da Birtaniya da kuma Denmark baya ga attajiran kasashen Norway da Austria da Holland da kuma Iran.