Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya ce zasu bi hanya ɗaya domin warware rikicin da ya addabi jam’iyyar PDP.
Ɗan takarar ya kuma sha alwashin cewa zai baiwa mara ɗa kunya idan har ya zama shugaban Najeriya a zaben 2023.
Wannan ne zuwa yayin da NEC ta kaɗa kuri’ar amincewa da Ayu a matsayin shugaban PDP na ƙasa.
Ɗan takarar shugaban ƙasa a inuwar jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya sha alwashin cewa zai baiwa maraɗa kunya idan aka zaɓe shi shugaban ƙasan Najeriya a 2023.
Premium Times ta ruwaito cewa Atiku ya faɗi haka ne yayin da yake jawabi a taron majalisar zartarsa (NEC) karo na 97 a birnin tarayya Abuja ranar Alhamis.
Ya kuma yaba wa mambobin NEC bisa namijim kokari da goyon bayansu yayin babban taro na musamman wanda ya lashe tikitin takarar shugaban ƙasa a watan Mayu.
“Ba zan iya gode muku yadda ya kamata ba, alƙawarin da zan ɗaukar muku shi ne zan ba maraɗa kunya game da tsammanin da kuke mun da burin yan Najeriya a kaina.”
“Bari na yi amfani da wannan damar na kara gode wa shugaban BoT mai barin gado bisa sadaukarwarsa da fifikon da ya nuna wa jam’iyyar mu.” – Atiku Abubakar.
Yadda zamu magance rikicin cikin gida a PDP – Atiku
A ruwayar Punch, Tsohon mataimakin shugaban ƙasa ya bayyana shirinsa na warware duk wasu ƙulli da suka hana jam’iyyar PDP zaman lafiya a cikin gida.
“Masu magana sun yi tsokaci kan rikicin iyali ɗaya, saɓanin iyali abu ne da ya saba faruwa ko Iyalai na jini ɗaya haka zalika iyalin da siyasa ta haɗa su.”
“Amma ina mai baku tabbacin cewa mun shirya warware matsalolin nan a cikin gida, babu wata matsala muhimmiya, abu ne da ya saba faruwa.”
Bugu da ƙari, Atiku ya yi kira ga mambobi su tabbatar babu wata hanya da suka bi face ta cikin gida wajen warware rikicin kana su kiyaye tanade-tanaden kundin dokokin jam’iyya.
A wani labarin kuma An Naɗa Sabon Shugaban BoT Na Ƙasa Bayan Walid Jibrin Ya Yi Murabus Yau a Abuja Shugaban kwamitin amintattu na jam’iyyar PDP ta ƙasa (BoT), Sanata Walid Jibrin, ya sauka daga kan muƙaminsa.
Bayanai sun nuna cewa an naɗa Sanata Adolphus Wabara, tsohon shugaban majalisar Dattawa a matsayin muƙaddashin shugaba.
Source: LEGITHAUSA