Dan takarar shugabancin kasa a Najeriya a Jam’iyyar PDP Atiku Abubakar ya ce yana tunanin bai wa Yankin Naija Delta izinin mallakar daukacin dukiyar man da ake hakowa sabanin kashi 13 da ake basu.
A wata hirar da yayi da ‘The Africa Report’ da aka wallafa ranar laraba, Atiku Abubakar yace bashi da wata damuwa barin yankin ya mallaki dukiyar da yake da shi, sai dai kawai zai dorawa yankin harajin da zai dinga biya ga gwamnatin tarayya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana takaicin sa da yadda ake baiwa yankin kashi 13 kacal na arzikin man da ake sayarwa, yayinda a Jamhuriya ta farko kashi 50 ake basu.
Sai dai yace bukatar sa ba za ta samu ba dole sai an sake fasalin dokokin kasar ta hanyar lalama da kuma tattaunawa da sauran jama’a.
A wani labarin na daban kuma Tsohon shugaban Najeriya, Olusegun Obasanjo ya ce, ya sauya matsayinsa na rashin goyon bayan tsohon mataimakinsa, Atiku Abubakar a zaben 2019.
Mr. Obasanjo ya bayyana haka ne bayan ziyarar da Atiku Abubakar da wasu jiga-jigan jam’iyyar PDP suka kai masa a gidansa da ke birnin Abeokuta.
Obasanjo ya ce, ya yi amanna cewa, Atiku ya daidaita kansa kuma a yanzu haka ya cancanci samun goyon bayansa a zaben kasar mai zuwa.
Tsohon shugaban na Najeriya ya taya murna ga Atiku game da nasarar da ya samu ta wakiltar jam’iyyar PDP a zaben shugaban kasa, in da zai fafata da shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC.
A can baya dai, Obasanjo ya lashi takobin rashin mara wa Atiku baya wajen fafutukarsa ta ganin mafarkinsa na zama shugabban kasa ya zama gaske.
An dai jiyo tsohon mataimakin shugaban kasan yana cewa abu ne mai sauki ya kayar gwamnatin buhari ko dan takarar APC a zabe mai zuwa.
Tsohon shugaban kasar ya bayyana kwarin gwuiwar da yake dashi domin tunkarar zaben 2023