A yayin da aka bayyana sakamakon zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar, dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar, ya samu rinjaye akan takwarorinsa na jam’iyyar APC Bola Tinubu da na Labour Party (LP) Peter Obi, yayin da sakamakon zaben ya fara fitowa daga kananan hukumomin jihar Akwa Ibom.
A yayin da aka bayyana sakamakon kananan hukumomi 21 a cibiyar tattara sakamakon zaben shugaban kasa a karkashin jagorancin kwamishinan zabe na jihar, Dr. Cyril Onoregbe, Atiku ya ya samu nasara a kananan hukumomi 17, inda Tinubu ke da uku, yayin da Obi ya samu nasara a karamar hukuma daya.
A cewar mai tattara sakamakon zaben, Zaben da aka gudanar a wasu Unguwanni bai kammala ba, sabida tashe-tashen hankula musamman a kananan hukumomin Ikono, Etim Ekpo, Ini da sauran kananan hukumomin, inda jami’an suka samu labarin sace na’urar BVAS da kashe-kashe.
A wani labarin na daban jam’iyyar Labour (LP) ta yi kira da a soke zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a jihar Ribas.
A cewar jam’iyyar Labour, ta yi matukar kaduwa da labaran da ke fitowa daga jihar Ribas bayan zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar a ranar Asabar.
Wata sanarwa da shugaban jam’iyyar Labour ta kasa Barr Julius Abure ya fitar, ta ce ‘yan bangar siyasa da ake kyautata zaton gwamnatin jihar ne suka turoso, sun mamaye rumfunan zabe da wuraren tattara sakamakon zabe, inda suka kwace kayan zabe da suka hada da takardar sakamakon zabe, suka daura sakamakon zabe na jabu a na’urar BVAS.
Source:LeadershipHausa