An samu wasu ‘yanuwan Gwamna Aminu Waziri Tambuwal da suka fice, suka bar shi a jam’iyyar PDP.
Habibu Waziri Tambuwal wanda yana da mukami a gwamnatin jihar Sokoto, ya dawo APC mai mulkin kasa.
Isah Sadik Achida yace Alhaji Kabiru Moyi da aka sani a PDP yana tare da ‘dan takaransu, Ahmad Aliyu.
A jihar Sokoto, Aminiya ta kawo rahoto wasu daga cikin ‘yanuwan Aminu Waziri Tambuwal sun sauya-sheka daga jam’iyyar APC zuwa PDP.
Wannan labari da ba za iyi wa PDPn dadi ba, ya fito ne daga bakin Shugaban jam’iyyar APC na reshen Jihar Sokoto, a ranar Juma’a, 4 ga watan Nuwamba 2022.
Isah Sadik Achida ya shaidawa ‘yan jaridar cewa Alhaji Kabiru Moyi da Habibu Waziri Tambuwal sun shigo jam’iyyarsu ta APC mai mulkin Najeriya.
Shugaban APC yace sun shafe sama da shekara guda su na damawa da Kabiru Moyi a jam’iyya, sai yanzu aka gan shi tare da ‘dan takararsu na Gwamna.
A cewar Isah Achida, haduwar Moyi da ‘dan takaran APC, ya nuna ‘dan siyasar ya bar PDP. Rahoton yace an yi ta ce-ce-ku-ce bayan ganin ‘yanuwan.
Mai girma Gwamna watau Aminu Tambuwal da Ahmad Aliyu mai neman gaje kujerarsa a APC.
Moyi bai amfana da PDP ba?
Wani na kusa da Kabiru Moyi wanda ya tabbatar da abin da jam’iyyar APC ta fada, yace ‘dan siyasar ya fice daga PDP ne saboda Gwamna bai taimaka masa ba.
Shi kuwa Habibu Waziri Tambuwal yana cikin masu kusanci da Tambuwal, baya ga haka Darekta ne shi a gwamnatin Sokoto, amma aka ji ya shiga jam’iyyar APC.
Habibu Waziri Tambuwal ta fi ba magoya baya da masu bibiyar siyasar jihar Sokoto mamaki, ganin alakarsa da Gwamna kuma babban jagora a PDP.
PDP ta rasa mabiya a Tambuwal Wata majiya tace sauya-shekar wadannan ‘yan siyasa ya yi sanadiyyar da mabiyansu a garin Tambuwal suka fice daga jam’iyyar PDP mai rike da jihar.
Hakan zai zama illa ga Gwamna Tambuwal, ganin shi ne Darekta Janar na kwamitin zaben Atiku Abubakar a karkashin PDP a 2023, kuma abin alfahari ga APC.
Ba a iya samun Kabiru Moyi da Habibu Tambuwal domin jin abin da ya fitar da su daga PDP ba. Ita ma jam’iyyar PDP ba tayi magana a kan wannan lamari ba.
Rikicin APC a Kano A gefe guda, an samu labari cewa Hon. Alhassan Ado-Doguwa ya zargi shugabannin APC na jihar Kano da yin watsi da wasu ‘yan jam’iyya a shirin 2023.
‘Dan majalisar yace Murtala Sule Garo yana goyon bayan Atiku Abubakar a kan ‘dan takaran APC watau Bola Tinubu saboda surukutunkar da ke tsakaninsu.
Source:legithausang