Jam’iyyar APC mai mulkin Najeriya ta tsayar da ranar 26 ga watan Maris na wannan shekara domin gudanar da taronta na kasa domin zaben shugabannin da za su jagorance ta.
Da farko dai, sanarwar da jiga-jigan jami’iyyar ta APC suka fitar a yau Litinin ta ce, an fasa gudanar da taron har sai baba-ta-gani.
Wannan na zuwa ne bayan rahotanni daga Abuja sun ce, gwamnonin jam’iyyar sun gudanar da taro domin dinke barakar da aka samu da kuma matakan da suka dace wajen sasanta ‘yayan jam’iyar da aka batawa lokacin da aka gudanar da zaben shugabanni a matakan jihohi.
Wasu daga cikin ‘yayan jam’iyyar sun yi barazanar zuwa kotu domin kalubalantar shugabannin rikon saboda abinda suka kira gazawar da suka yi na shirya taron kasa domin zaben shugabannin gudanarwar jam’iyyar tasu.
Masu sanya ido akan siyasar Najeriya na kallon wadannan matsaloli a matsayin zakaran gwajin dafi ga jam’iyyar mai mulki musamman ganin yadda aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin ‘yayan ta a daidai lokacin da ake shirin tinkarar zaben shekara mai zuwa.
A wani labarin na daban Masu aikin ceto a Brazil na cigaba da neman masu sauran rai cikin laka da baraguzan gine-gine, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa, da zabtarewar kasa a birnin Petropolis, a daidai lokacin da kawo yanzu adadin wadanda suka mutu a iftila’in ya karu zuwa mutane 117
Guguwar dai ita ce ta baya bayan nan da ta afkawa Brazil cikin watanni ukun da suka gabata, masifun da masana suka ce sauyin yanayi ne ke kara ta’azzara su.
A halin da ake ciki, gwamnatin jihar ta Petropolis ta ce an ceto akalla mutane 24 da ransu.
Da farko an ce, ana fargabar kimanin mutane 300 sun bace sakamakon wannan ibtila’in na ranar Taklatar nan.
Masana sun bayyana cewa, ruwan da aka tafka na tsawon sa’o’i uku, yawansa ya yi daidai da ruwan sama na tsawon wata guda.