Jam’iyyar APC a Jihar Taraba ta kori dan takararta na gwamnan jihar a zaben 2023 da aka kammala, David Sabo Kente kan zargin yi mata zagon kasa.
Har wa yau, jam’iyyar ta kori zababben Sanatan Taraba da Kudu, David Jimkuta sakamakon zarginsa shi ma da yi mata zagon kasa a lokacin zabukan da aka kammala na 2023.
Shugaban jam’iyyar na jihar, Elsudi Ibrahim ne ya bayyana a haka a wajen taron manema labarai da ya gudanar a Jalingo babban birnin jihar.
Mista Elsudi ya ce Sabo Kente ya daina daukar kansa a matsayin memba na jam’iyyar.
Elsudi ya jaddada cewa har yanzu shi ne halastaccen shugaban jam’iyyar na jihar, kamar yadda kotu ta tabbatar, bayan ce-ce-ku-cen da ya biyo bayan kuri’ar yankan kauna da wasu membobin kwamitin gudanarwar jam’iyyar suka kada masa.