Ranar Laraba ce Jam’iyyar (APC) ta gode wa ‘yan Nijeriya dangane da nasarar da Bola Ahmed Tinubu, ya yi wajen lashe zaben Shugaban kasa wanda aka bayyana sakamakon shi ranar Talata.
Zabebban Shugaban ya gode wa ‘yan Nijeriya inda ya ce hakan ta kasance ne saboda kwarin gwiwar da suke bashi, da soyayyar da suke nunawa kasarsu.
Sakataren hulda da jama’a na jam’iyyar APC Felid Morka ya bayyana haka a Abuja lokacin da yake taya Mista Tinubu da mataimakinsa Kashim Shettima, a kan nasarar lashe zaben da suka yi.
Mista Tinubu ya samu kuri’u milyan 8,794,726 wanda hakan ne ya bashi damar lashe zaben Shugaban kasa da aka yi ranar 25 ga Fabrairu.
Ya kada sauran ‘yan takarar da suka hada da Atiku Abubakar, na jam’iyyar (PDP)wanda ya samu kuri’u 6,984,520 , sai Peter Obi na jam’iyyar Labour Party (LP) 6,101,533 a zaben.
Mista Morka ya godewa ‘yan Nijeriya kan gaggarumin gudunmawar da suka ba dan takarar jam’iyyar APC , zaben an fafata shi ne a duk fadin Nijeriya a tarihin siyasar Nijeriya.
Ya cigaba da bayanin “ Kasarmu da siyasarmu sun kara bunkasa tare a kokarin da ake yi na cimma muradan cigaban cigaban kasa baki daya.
“Ga shugaban jam’iyyarmu Shugaban kasa Muhammadu Buhari muna nuna goiyarmu akan kyawawan abubuwan cigaban da yayi da suka kasance wata madafar da dantakararta ya bi wajen samun nasara.
Suma jami’an tsaro baimanta dasu ba domin kuwa ya godewa irin gudunmawar suka bada wajen ayyukan da suka yi na tabbatar da zaman lafiya, da kuma bin doka da oda.
Source:Leadershiphausa