Jam’iyyar adawa ta APC ta bukaci gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf na Jihar Kano da ta kara wa’adin kwace wasu kadarori da rusa wasu a jihar zuwa wasu da uban gidannsa Rabi’u Kwankwaso ya sayar.
Abba ya kasance mataimaki na musamman kuma daga baya ya zama kwamishinan Kwankwaso lokacin yana gwamnan jihar tsakanin 1999 zuwa 2003 da 2011 da 2015.
Kasa da sa’o’i 72 da rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu, Abba ya ba da umarnin rusa wasu kadarorin da ya yi ikirarin cewa gwamnatin da ta gabata ta sayar da su ba bisa ka’ida ba.
Ya kuma yi ikirarin cewa an gina wasu kadarori a filayen gwamnati ba bisa ka’ida ba.
Tsakanin Asabar da Talata, gwamnati ta rushe gine-gine akalla guda hudu.
A ranar Asabar din da ta gabata ma an rushe wani gini mai hawa uku mai shaguna 90 a yankin Nassarawa da ke jihar.
A wannan rana ne gwamnatin ta rushe Otal din Daula, otal din da gwamnatin Ganduje ta sayar tare da sake ginawa a karkashin tsarin hadin gwiwar wasu ‘yan kasuwa.
Gwamnatin ta kuma rushe wani gini a sansanin Alhazan jihar.
A ranar Litinin ne gwamnatin ta rushe shaguna a kasuwar Kantin Kwari; ta yi ikirarin cewa an gina shagunan ne a kan wani fili da aka sayar ba bisa ka’ida ba.
Sauran wuraren da aka ruwaito cewa an sawa jan fenti sun hada da Kasuwar Siyayya ta Shahuci, tsohon ginin Kamfanin jarida na Triumph, wanda aka sayar wa ‘yan kasuwa.
“Kaddarorin gwamnati a lamba 5, 6, da 7 a kan titin Bala Muhammed. Kadarorin gwamnati mai lamba 132 da ke titin Dawaki da lamba 13 a titin Ali Akilu gwamnatin Kwankwaso ce ta siyar da su.
“Kaddarorin gwamnati da ke lamba 193 da 194 da 196 da 197 da 198 da 920 duk a titin Ahmadu Bello gwamnatin Kwankwaso ce ta siyar da su, haka kuma Gwamna Ganduje ya yi amfani da su,” in ji Iliyasu.
APC ta yi ikirarin cewa Abba ne sakataren Kwankwaso, lokacin da aka sayar wadannan kadarorin.