Matakin da jam’iyyar APC mai mulki ta dauka na ayyana Honarabul Abbas Tajuddeen daga Jihar Kaduna a matsayin wanda take so ya zama shugaban majalisar wakilai da Ben Kalu daga Jihar Abia a matsayin mataimakinsa ya bar baya da kura.
A ranar Litinin ne jam’iyyar ta fitar da sunayen ‘yan majalisar dokokin da ta ke so su zama shugabannin majalisun dokoki ta 10 bayan da, a cewarta, ta tuntubi zababben shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
A bangaren majalisar dattawa, APC ta zabi Sanata Godswill Akpabio da Barau a matsayin wadanda take su zama shugaba da mataimakinsa.
Sai dai matakin da ta dauka a majalisar wakilai bai yi wa wasu manyan ‘yan majalisa dadi ba, abin da ake gani zai iya haddasa rikici.
Tuni wasu daga cikin wadanda suke zawarcin kujerar suka hau dokin na-ki, inda suka yi watsi da matakin jam’iyyar.
Wadanda suke zawarcin kujerar shugaban majalisar tarayyar da suka ki amincewa da wannan mataki sun hada da Honarabul Idris Wase da Alhassan Ado Doguwa da Sada-Soli Jibiya.
Sauran sun hada da Honorabul Mukhtar Betara da kuma Ahmed Jaji.
Wasu daga cikin zababbun ‘yan majalisar wakilan wadanda suka nuna rashin jin dadinsu dangane da matakin jam’iyyar APC sun gudanar da wani taro a Abuja a ranar Litinin.
Sun kwatanta wannan mataki da uwar jam’iyyar ta dauka a matsayin yunkurin yi musu dauki-dora.
Cikin mahalarta taron har da Honarabul Wase da Ado Doguwa da Yusuf Gagdi and Sada-Soli da Mohammed Monguno.
Honorabul Wase shi ne mataimakin kakakin majalisar tarayya, kuma ya bayyana cewa wanda jam’iyyar APC ta zaba, Abbas Tajuddeen, ba mutum ba ne da ‘yan majalisa suka sani sosai.
Ya caccaki matakin da APC ta dauka, inda ya ce bai kamata a dauki irin wannan mataki ba tare da tuntubar masu ruwa da tsaki ba.
Shi ma Alhassan Ado Doguwa, wanda a yanzu shi ne shugaban masu rinjaye, ya bayyana cewa dole ne a bar majalisar ta rika zabar shugabanninta.
Ya bayyana cewa hakkinsu ne zabar shugaba a majalisa kuma bai kamata wasu daga waje su rika zaba mata shugaba ba.
“Wani sako da nake son aikawa shi ne majalisa wuri ne da dole ne a bari ya rinka zaba wa kansa shugaba. Batun wanda zai jagorance mu, wata matsala ce wadda ta shafe mu, mu kadai ba matsalar wani ba ce,” in ji Doguwa.