Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar ya yi zargin cewa jam`iyyar APC mai mulki na amfani da bangaren shari`a da nufin murkushe jam’iyyun hamayya.
Mataimaki na musaman ga dan takaran shugaban kasar, Mallam Abdurrashid Shehu ya bayyana wa manema labarai cewa Jam’iyyar APC na kokarin karya dimokradiyya kasar nan.
Tsohon mataimakin shugaban kasar, ya yi misali da hukuncin da kotunan daukaka kara suka a yanke a wasu jihohi, ciki har da Zamfara da Filato da Kano da Nasarawa, inda ya bayyana cewa gwamnati na hada kai ne da shari`a wajen kwace jihohin da ke karkashin ikon jam’iyyun adawa.
Atiku Abubakar ya ce sun lura da take-taken jam’iyyar APC kuma sun fahimci cewa da sannu tana nema ta murkushe dimokuradiyya baki daya.
Tsohon mataimakin shugaban kasar ya yi zargin cewa APC na amfani da karfi wajen yin magudi ko fakewa da bangaren shari’a wajen soke nasarar da `yan hamayya suka samu a wasu jihohi.
”Wannan bangare na sharia, bangare ne da yake cin gashi kansa amma yadda mu ke zargin sun yi kutse wajen shiga wannan bangare tare da yin kokari da yukurin karbar wasu jihohi, idan ka duba jihohi ne da suka fito daga jam’iyyun hammaya”, in ji shi.
Sai dai jam’iyyar APC ta musanta wannan zarge-zarge daga Atiku.
Jam’iyyar mai mulki ta ce kalaman na Atiku ba komai ba ne face zafin radadin faduwa zabe ke damunsa.

Source: LEADERSHIPHAUSA