Wata babbar kotu a jihar Kano ta bayar da sanarwar dakatar da Sufeto Janar na ‘yan sanda da Mataimakin Sufeto Janar na shiyyar ta 1 Kano, da kwamishinan ‘yansandan Kano daga gayyata ko kama shugabannin jam’iyyar APC na mazabar Ganduje da ke karamar hukumar Dawakin Tofa.
Idan za a iya tunawa LEADERSHIP HAUSA ta rawaito muku cewa wasu da suka kira kansu shugabannin jam’iyyar APC a matsabar Ganduje sun dakatar da shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, wanda jam’iyyar a matakin jihar ta soke takatarwar.
Tun daga nan ne ‘yan jam’iyyar a matsabar suka dauki matakin shari’a, inda suka nemi kotu ta tabbatar da dakatarwar da suka yi wa Ganduje.
A wani labarin na daban ayan ‘yan watanni da nada shi a matsayin mukaddashin darakta-janar na hukumar kula da zirga-zirgar jiragen saman Njeriya, (NCAA), Kyaftin Chris Najomo, na fuskantar zargin kashe kudi ba bisa ka’ida ba, da keta dokokin gwamnati.
Jaridar Daily Nigerian ta ruwaito cewa, babban jami’in kula da harkokin sufurin jiragen sama bayan nada shi a mukamin mukaddashin hukumar a ranar 13 ga Disamba, 2023, Najomo ya kashe makudan kudade, inda ya sayi wata mota kirar Toyota Landcruiser 2022 da ta haura N250m, wacce ko a cikin kasafin kudin bana ba a saka ta ta ba.
Wani mai mutum da aka sakaya sunansa ya kuntsawa jaridar Daily Nigerian cewa babu inda Majalisar Dokoki ta amince masa a kunshin kasafin kudin NCAA na ya sayo wannan mota ta musamman.
DUBA NAN: Kotu A Kano Ta Dakatar Da Ganduje Daga Shugaban Jam’iyyar APC
Hakazalika binciken Daily Nigerian ya nuna cewa an sayo motar SUV ne ba tare da amincewar hukumar kula da saye da sayar da kayayyaki ta kasa da majalisar zartarwa ta tarayya ba.