Wani rahoto da BBC ta yi kan wata ɓaraka da ta kunno kai a jihar Kaduna tsakanin wasu ‘ya’yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar dangane da rabon muƙamai a matakin gwamnatin tarayya da na Jiha.
Wasu magoya bayan jam’iyyar a yankunan karkara na zargin cewa ana nuna musu bambanci wajen rabon mukamai, duk kuwa da irin gudunmuwar da suka ce sun bayar a lokacin zaɓe.
Mutanen sun kafa hujja da wasu manyan muƙamai huɗu da suka ce an ba wa wata ƙaramar hukuma guda.
Alhaji Yusuf Owner Dutsen Wai, na ɗaya daga cikin ‘ya’yan jam’iyyar APC da ke zargin cewa ba a yi musu adalci ba wajen rabon, ya kuma shaida cewa su mutanen karkara ba a yin komai da su.
Ya ce, ‘‘Mun tura mota ne ta bar mu da hayaƙi saboda dukkan muƙaman nan da aka bayar babu wani ɗan karkara ko guda.”
‘‘ Tun daga kan muƙamin minista har zuwa sauran muƙamai an raba wa waɗanda ba su iya cin akwatunan zaɓensu ba, idan har gaskiya ake so idan mutum ɗan jam’iyya ne ai sai a ɗauki muƙami a ba shi ba a dunƙule abu wuri ɗaya kamar ƙwallo ba,” in ji shi.
Shi kuwa Honorabul Umar Sale Koch, daga yankin Kujama na jihar ta Kaduna, shaida wa BBC ya yi cewa, idan har jam’iyyar APCn ba ta ɗauki mataki na waiwayar yankunan karkara wajen rabon muƙaman ba, to hakan ka iya zama barazana ga jam’iyyar tasu a nan gaba.
Ya ce,“ Siyasa aba ce ta jama’a kuma har aka ci gaba da kasancewa a wannan yanayi to zai iya zama barazana ga jam’iyyarmu ta APC, domin yawan ƙuri’u da jama’ar ake samu daga karkara za su ƙaurace wa jam’iyyar.”
Dan siyasar ya ce,“ Idan aka kalli siyasar ma a yanzu gaba ɗayan waɗanda suka fito daga wata jam’iyyar suka yake mu yanzu sun dawo kuma su ne suke ta wawushe muƙaman, mu muna tsaye mun zama ‘yan kallo.”
To sai dai a nata ɓangaren jam’iyyar APC a jihar ta Kaduna ta ce kamata ya yi masu irin wannan ƙorafi su kwantar da hankalinsu kasancewar gwamnatin APCn a matakin tarayya da kuma jiha ta ƙuduri aniyar tafiya tare da kowa.
Honorabul Salisu Tanko Sono, wanda shi ne kakakin jam’iyyar APC a Kaduna, ya ce, ya kamata mutane su rinƙa haƙuri domin ita gwamnati tana da faɗi, kuma mukaman nan yanzu aka fara, mutanen da suke ganin ba a yi da su, su yi haƙuri ana sane da su.
Taƙaddama tsakanin ‘yan siyasa a Nijeriya ba sabon abu ba ne, inda a wasu lokutan har takan kai a samu rarrabuwar kai a tsakanin ‘ya’yan jam’iyya.
Source LEADERSHIPHAUSA