Ana Sa Ran yau Laraba Mai Mala Buni Zai Dawo Najeriya.
A daidai wannan lokaci da ake ta cece-kuce kan shugabancin rikon Jam’iyyar APC na kasa, muke samun labari cewa zuwa gobe ne ake sa ran dawowar gwamna Mai Mala Buni wanda ake ikirarin an sauke daga shugabancin CECPC.
Masu hasahen suna nuna cewa idan tsohon shugaban rikon kwaryan ya dawo Najeriya daga birnin Dubai, za a kawo karshen rikicin shugabancin Jam’iyyar wanda aka fara a jiya.
A jiya aka ji cewa jam’iyyar APC ta musanya sauyin shugabanta, ta ce har yanzu Mai Mala Buni ne yake rike da CECPC, ta ce mutane su yi watsi da labaran da ke yawo.
Sanarwar ta fito ne daga bakin sakataren rikon kwarya, Sanata John James Akpanudoedehe. Ba a dade ba sai aka ga Abubakar Sani Bello a kan kujerar Mai Mala Buni.
Hajazalika
Rudanin APC: An ce sakataren riko na APC na kasa yayi murabus, amma ya musanta batun
Yayin da inuwar jam’iyyar APC ke ci gaba da dumama, sakataren riko na jam’iyyar ya lallaba ya fice daga cikinta Har yanzu dai ba a san dalilin ficewarsa ba, amma ana danganta matakin nasa da rikice-rikicen da jam’iyyar ke fuskanta Idan baku manta ba, a jiya ne gwamnan jihar Neja ya dale kujerar gwamnan Yobe ta shugabancin jam’iyyar
Sakataren kwamitin rikon kwarya na jam’iyyar APC mai mulki ta kasa, Sanata John James Akpanudoedehe, ya yi murabus daga kan kujerarsa. Jaridar Leadership ta tattaro cewa, tuni Akpanudoedehe ya kwashe dukkan kayan sa daga sakateriyar jam’iyyar ta kasa da ke titin Blantyre, Wuse 2 a babban birnin tarayya Abuja.
Duk da cewa ba a san dalilan da suka sa ya fice daga jam’iyyar ba nan take, amma an gano cewa matakin nasa bai rasa nasaba da yadda ake tafiyar da jam’iyyar ba, inda wasu gwamnonin suka yi yunkurin tsige shi.
READ MORE : Shugaban yan ta’adda ya kashe daya daga cikin mabiyan shi.
Duk da cewa jami’an jam’iyyar da dama sun tabbatar da cewa Akpanudoedehe ya kwashe kayayyakinsa daga ofishinsa, amma ba su iya tabbatar da ganin wasikar da ke nuna ficewarsa ba, inji rahoton Vanguard.
Shi ma Sanata Akpanudoedehe bai amsa kiran da aka yi masa ba domin jin ta bakinsa game da batun na murabus dinsa.
Ban yi murabus ba
Sai dai, a wata hira da jaridar Daily Trust, ya ce shi sam bai yi murabus ba. A cewarsa: “Na kiaranta a kafafen sada zumunta cewa na yi murabus daga mukamin sakataren jam’iyyar APC.
Ina so in bayyana cewa ba gaskiya ba ne; cewa ban yi murabus ba. Idan na yi murabus, da kun ga takardar murabus da na rubuta.
Wani ba zai ce wani ya mutu ba sa’ad da yake raye.
Ban fi jam’iyya girma ba, ko shugaban kasa wanda shi ne jagora a kasa ba. Ina jiran shugaban kasa ya dawo.”