Wasu ‘yan bindiga sun kashe wani jami’in dan sanda tare da yin sace gami da garkuwa da wasu ‘yan kasar China biyar da ke aiki a wata mahakar zinari a gabashin Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango, kamar yadda majiyoyin soji suka bayyana.
Kakakin rundunar sojojin yankin Manjo Dieudonne Kasereka ya bayyana cewa, da misalin karfe biyu na safe, wasu ‘yan bindiga dauke da makamai suka kai wa sansanin ‘yan kasar China hari a kauyen Mukera da ke yankin Fizi na lardin Kivu ta Kudu.
Jami’in yace “’Yan kasar China 14 ne ke sansanin, kafin maharan suka sace biyar kuma su tafi da su zuwa wani wuri da ba a sani ba”, inda aka kwashe sauran tara zuwa tudun muntsira.
Kanal David Epanga, shugaban rundunar soji a Fizi, ya ce dan sanda daya ya rasa ransa a harin.
Ma’aikatan ‘yan kasar China biyar da aka sace ma’aikatan wani kamfani ne da ke aikin hakar gwal a yankin tsawon watanni hudu zuwa biyar, in ji shugaban kungiyoyin fararen hula na Fizi Lusambya Wanumbe.
A wani labarin na daban kuma hukumomi a Jamhuriyar Dimokaradiyyar Congo sun ce Fararen hula 19 ne ‘yan tawayen Uganda suka daddatse tare da kone su har lahira.
Wani basaraken yanki ya ce jami’an kungiyar agaji ta Red Cross ne suka gano gawarwakin a yayin da suka shiga daji don neman wadanda suka bace a yayin harin da aka kai kauyen Kasanzi da ke yankin Beni a arewacin Kivu.
Beni na tsakiyar yankin da kungiyar ‘yan tawaye ta Allied Democratic Forces (ADF), mai nasaba da ISIS ta ke kai munanan hare hare duk matakin dokar ta baci da shugaba Felix Tshisekedi ya dauka.