Uban kasa a jihar Kano, Alhaji Tanko Yakasai ya bayyana cewa sam bai dace ba Arewa ta nemi shugabancin Najeriya a shekarar 2023.
Ya bayyana cewa kamata yayi Arewa ta bar kudu ta nemi shugabancin Najeriya a zabe me zuwa.
Atiku, Kwankwaso, Tambuwal na daga cikin wanda ke neman shugabancin Najeriya.
Saidai Tanko Yakasai yace me Arewa zata nuna tace a zabeta a shekarun da ta yi tana mulki?
Yace tunda Arewar ta yi, kamata yayi ta bar kudu itama ta yi.