Shugaban Afrika ta Kudu Cyril Ramaphosa ya kori Ministar Kula da Yawon bude idanu ta kasar, bayan ta caccaki tsarin tafiyar da shari’a na kasar a wani abu mai kama da hukunta masu niyar yin hakan a nan gaba.
Minista Lindiwe Sisulu wadda ‘ya ce ga tsaffin yan gwagwarmayar fatattakar fararen fata daga kasar Walter da Albertina Sisulu, ta fara caccakar tsarin tafiyar da shari’ar kasar da kuma baki daya kundin tsarin mulkin kasar.
Minista Sisulu na ganin cewa, akwai tarin kura-kurai a kundin tsarin mulkin kasar wadanda har yanzu suke nuna wariya ga bakaken fata da gwamnatin kasar ta ki yarda a cire, yayin da ake ci gaba da bai wa dai-daikun fararen fatar da suka rage a kasar fifiko a wasu fannonin.
Sai dai masu fashin baki na ganin cewa, Sisulu na wadannan maganganu ne saboda tana da sha’awar tsayawa takarar shugabancin kasar karkashin jam’iyyar ANC.
To amma dai tuni shugaban kasar, Ramaphosa ya taka mata burki, kan abin da ya kira cin zarafin ‘yancin kasar da kuma darajar tarin shari’ar kasar.
Sai dai wasu na ganin an kori ministar ne saboda wasu daalilai da ba’a bayyana ba yayin da wasu ke ganin an kori ministar bisa ka’ida.