Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da kama wasu mutane tara da ake zargi da nuna tutocin kasar Rasha a Maiduguri.
Rundunar ‘yan sandan ta kara da cewa za ta ci gaba da sanya ido da kuma sintiri a yankin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a a duk fadi garin Maiduguri.
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno ta tabbatar da kama wasu mutane tara da ake zargi da nuna tutocin kasar Rasha a Maiduguri.
Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Yusuf Lawal ne ya bayyana haka a ranar Talata yayin da yake bayar da rahoton halin da ake ciki ga Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) a Maiduguri.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne a unguwar Zannari Tamsu da ke unguwar Gwange, Maiduguri a ranar 5 ga Agusta, 2024.
Lawal ya ce wadanda aka kama sun hada da Khalafi Abdulhamid, Mohammed Abubakar, Mohamed Ibrahim, da Abba Hassan dukkansu mazauna yankin Zannari Tamsu.
Duba nan: Dalilai 3 da bai kamata a manta da kutsen da Rasha ke yi wa Najeriya ba
“Bugu da kari, an kama wasu masu zanga-zanga biyar a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri, dauke da tutocin kasar Rasha.
“Wadanda ake zargin, Bashir Ahmad, Musa Lawan, Abba Mallam, Habibu Auwal, da Inusa Abdullahi, an mika su zuwa Crack Squad domin gudanar da bincike mai zurfi, tare da gurfanar da su a gaban kotu,” in ji shi.
Kwamishinan ya ce an kwantar da hankulan muzaharar inda ya ce ‘yan sanda za su ci gaba da sanya ido da kuma sintiri a yankin domin tabbatar da tsaron lafiyar jama’a.