Sheikh Ibrahim Zakzaky wanda shine jagora ‘yan uwa musulmi na najeriya a wani taron manema labarai daya gabatar a babban birnin tarayyar Abuja ya bayyana damuwar sa dangane da yadda mahukuntan najeriya suka rike fasfunan su na tafiya, shi da mai dakin sa malama zinatuddin wanda hakan ya kawo tsaiko a kokarin su na fita kasashen ketare domin neman magani sakamakon cutukan dake addabar su kuma likitocin cikin gida najeriya sun bayyana cewa babu kayan aikin da za’a iya musu aiki a cikin gida najeriya saboda hakanan dole a fita kasashen ketare.
Lamarin ya samo asali ne dai tun disambar 2015 inda sojojin nijeriya karkashin jagorancin janaral tukur yusuf buratai, shugaban sojin najeriya a wancan lokaci suka kai harin kan mai uwa da wabi a gidan jagoran ‘yan uwa musulmin kuma hakan yayi sanadiyyar mutuwar a kalla mutane daruruwa da kuma batan wasu da dama ciki har da ‘ya’yan sheikh zakzaky guda uku da kuma ‘yar uwar sa.
Sheikh zakzaky ya shafe tsahon shekara shidda yana tsare a hannun hukuma tattare da hukuncin kotu na a sake shi amma gwamnatin tarayya bata amsa wannan hukunci ba.
Daga baya malam zakzaky ya samu ‘yancin sa bayan da wata babbar kotun jihar kaduna ta wanke shi kuma ta sake shi amma sai dai bayan an sake shi sai gwamanti ta rike fasfo dinsa dana mai dakin sa wanda hakan ya haramta masa fita kasashen ketare domin neman lafiya kamar yadda likitoci suka bada shawara sakamakon munanan raunukan da suke jikin su shi da mai dakin sa wadanda suka samo asali tun harin kisan kiyashi da aka kai gidan shehin malamin a shekarar 2015, shekaru shidda da suka wuce.
An kiyasta fiye da mutum dubu wadanda ba’a gani ba tun bayan kisan kiyashin zariya kuma ana kyautata zaton duk an kashe su ne a gidan malamin dake gyallesu a zariya.